Jaruma mai tauraro, Hadiza Aliyu Gabon, ta taya diyar ta wanda ta karbi rainon ta murnar cika shekara biyar a duniya.

Hadiza Gabon ta karbi rainon Maryam Aliyu ne shekarun baya kuma tun lokacin shakuwar su na cigaba da kamari.

Ga masu bibiyan shafin ta na kafafen sadarwa, mawuyaci ne jarumar ta wallafa wani sako ko hoto a shafin ta ba tare da saka diyar ba.

Maryam wacce ta zama abokiyar wasan jaruma tayi murnar zagayowar ranar haihuwar ta ranar Lahadi 7 ga watan Disamba.

Hadiza ta raya wannan ranar tare da Maryam inda ta shirya mata shagulgula daban-daban cikin gida da makarantar ta

Ta kuma mamaye shafin ta na Instagram da hotunan mai bikin tare da rabuta sakonni masu sosa zuciya domin nuna farin cikinta da samun Maryam a rayuwar ta.

Cigaba da ayyukan taimako da take yi, jarumar ta kewaya da mai bikin wajen raba kayan tallafi ga nakasassu mara hali.

Yan uwa da kawayen jarumar sun taya Maryam murnar wannan ranar mai muhimmanci a gida da makarantar koyon karatun bokon ta.

Diyar ta kuma samu kyaututtuka na musamman daga Hadiza da kuma sauran kawayen ta.