ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Saraki ya gayyaci Emmanuella yar wasan barkwanci zauren majalisa domin tattauna kan yadda za'a bunkasa masana'antar nishadantarwa

Shugaban majalisar ya jinjina mata bisa sanarwa da tayi na cewa zata haska cikin wata sabuwar shirin fim da fitaccen Kamfanin dake fim wato Disneydake masana'antar Hollywood ke shiryawa

Shugaban ya sanar da sakon gayyatar ne a shafin sa na twitter da facebook ranar lahadi 18 ga wata. Yana neman matashiya da ta zo ta bada karin haske game da hanyar da za'abi wajen farfado da masana'antar nishadantarwa a kasar.

Wannan sanarwar tashi ya biyo baya bayan wata sanarwa da jarumar Emmanuella tayi na cewa zata haska cikin wani shirin fim wanda babban kamfani mai yin fina-finai wato Disney dake masana'antar Hollywood na kasar Amurka ke shiryawa.

Bisa wannan sanarwar tata shugaban majalisar dattawa ya jinjina mata bisa matsayin da ta samu tare da yi mata fatan nishadantar da jama'ar dake wancan masana'antar.

"Labarin ki mai dauke da darasi ne. Idan kin samu dama ki ziyarci zauren maalisar dattawa domin mu tattauna akan yadda zamu bunkasa basirar matasa a masana'antar nishadantarwa" Saraki ya rubuta.

ADVERTISEMENT

Ita dai wannan jarumar yar wasan barkwanci Emmanuell ta shahara ne bisa rawar da take takawa wajen bada dariya duk da cewa tana yar karama yar shekara bakwai.

Kalli bidiyon jarumar nan kasa:

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT