ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Saraki ya jagoranci zaman majalisa duk da tare hanya da yan sanda suka yi

Sai dai babu ingantaccen bayani kan yadda shugaban ya samu nasarar bayyana kansa a farfajiyar majalisar.

Jami'an sun tare duka hanyoyin shiga layin gidansa dake unguwar Maitama nan garin Abuja safiyar ranar talata 24 ga wata.

Kamar yadda hadimin sa ya sanar yan sandan sun tare shi ne yayin tafiya shelkwatar rundunar gomin amsa gayyatar da sufeton yan sanda ya tura masa kan batun barayin garin Offa.

A wani bangare kuma mun samu labari cewa, jami'an hukumar EFCC sun mamaye gidan mataimakin shugaban majalisar dattawa, Ike Ekweremadu, dake nan unguwar Apo tun da asuba.

ADVERTISEMENT

A jawabin sa wajen zaman majlisar Bukola Saraki ya bayyana cewa mataimakin sa bai samu damar halartar zaman yau ba domin jami'an DSS na tuhumar shi.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT