Kungiyar mai suna Plateau man of the year Awards cikin shirin ta na girmama manyan mutane yan jihar Filato da suke taka muhimmin rawa a fannoni daban daban don cigaban jihar, zata girmama jarumin bisa gudummawar sa ga cigaban harkar nishadantarwa a jihar.

Sani Mu'azu ya farin cikin sa bisa karramawar da za'ayi masa a wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na facebook tare da sanya hoton shi kamar yadda kungiyar ta fitar tare da jadawalin ranar bikin.

Za a yi bikin karramawar a ranar 23 ga Afrilu, 2018 a otal ɗin The Crest Hotel da ke Jos.

Jarumin, yana daga cikin tsofafin jarumai da suka raya masa'antar Kannywood. Shine kashin bayan kafa hadaddiyar kungiyar masu shirya fina-finai (MOPPAN).

Yana daga cikin jaruman kannywood da suke taka rawar gani a nollywood, ya fito a cikin fina-finan turanci da dama na masana'antar dake kudancin Nijeriya.