ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Sanata ya mayar ma gwamnatin tarayya martani da wannan hoton izgili kan karar da shigar a kan sa

Dan majalisar mai wakiltar yammacin jihar Kogi ya mayar da martani ga gwamnatin tarayya cikin izgili a wani sako da ya wallafa a shafin sa na kafar sada zumunta.

A karar da ofishin ma'aikatar shari'a na tarayya ta shigar ranar 31 ga watan janairu 2018, ana zargin Dino Melaye da bada shaidar karya ga mataimakin gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello mai suna Edward Onoja David tare da bada labari karya mara inganci.

A hoton za'a gan inda dan majalisar ya sa yatsan hannayen sa ga  idanuwa tare da rubuta "FG Vs Dino Melaye".

ADVERTISEMENT

Wannan ya nuna cewa dan majalisar ya shirya  damawa a gwamnati kan karar da ta shigar akan sa ko kuma izgili ne na tsokane wanda ya saba yi?

Idan ba'a manta ba bara wannan dan majalisar yayi kaurin suna a shafukan sada zumunta sakamakon bidiyon wakar izgilanci da ya fitar ga wadanda yake zargin cewa makiyan shi ne.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT