Ministan Buhari na kulle-kulle wajen ganin an tsige Bukola Saraki daga mukamin shi - Inji Sanata

Dan majalisar mai wailtar jihar Bauchi yace kulle-kulle ya faru ne tun lokacin da aka tafi hutun kirismeti da ta sabuwar shekara.

Dan majalisar dantawa Isa Misau yana zargin wani ministan shugaba Buhari da yin bita-da kulli domin a tsige shugaban majlisar datawa Bukola Saraki daga mukamin shi.

Sanata Misau yayi wannan korafin yayin da yake bayani a zauren majalisar dokoki ranar laraba 17 ga watan janairu 2018.

Dan majalisar mai wailtar jihar Bauchi yace kulle-kulle ya faru ne tun lokacin da aka tafi hutun kirismeti da ta sabuwar shekara.

"Sanda muka tafi hutu wasu mutane sun yi kokari tsige shugaban  majalisar dattawa a bayan fage."ya bayyana a zauren.

Sanata Misau yace dalilin da ya sanya ake kokarin tsige shugaban shine don ana sa ran cewa zai sauya sheka zuwa jam'iyar adawa ta PDP.

Ciki bacin rai yana mai cewa; "a lokacin hutun, wani minista yake jagorantar wannan yunkurin. Dalilin shi shine don ana sa ran cewa shugaban majalisar zai fice daga APC don haka suke ganin cewa ya kamata su janyo masa matsala. Shin wani irin kasa ne wannan? komai sai a danganta ta da adini ko kabila.

Yace an nada wasu ba tare da sun cancanta ba

Hakazalika Sanata ya tofa albarkacin bakin shi game da nada wasu mutane wadanda basu cancanta ba a wasu ma'aikata masu muhimmanci.

"Mafi yawancin mukamai da gwamnatin nan ta bayar ba bisa cancanta aka bayar dasu. Wasu mutanen sun mamaye ayyukan gwamnatin kamar sun fi shugaban kasa wajen bada umarni" ya kara.

Dan majalisar wanda a baya yayi fito-na-fito da sufeto yan sanda kan zargin yi ma hukumar jami'an tsaro zagon kasa ya nuna bacin ran sa game da yadda harkar shiri'a ke wakana a kasar duk da cewa gwamnatin na takama da taken yakin kawar da cin hanci da rashawa a kasar.

Sanatan ya soki babban alkalin kasa

Yace wadanda basu aikata laifin rawan gani ake gurfanar dasu a gaban kotu amma masu manya-manyan laifuffuka suna har yanzu ba hukunci da aka zantar masu.

Misalai da sanatan ya bayar game da rashin adalci a harkar shari'a shine batun tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal wanda kwamitin mataimakin shugaban kasa suka kama da laifi tare da takaddamar tsohon shugaban kwamitin gyaran fuska na hukumar fanshoAbdulrasheed Maina wanda babban alkali na kasa ke kokarin hana a tuhume shi.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

Clubless Super Eagles star Kelechi Nwakali surprisingly rejects ₦9.9million salary

Clubless Super Eagles star Kelechi Nwakali surprisingly rejects ₦9.9million salary

Burna Boy drops track list for upcoming album

Burna Boy drops track list for upcoming album

When and where to watch Super Eagles of Nigeria vs São Tomé and Príncipe

When and where to watch Super Eagles of Nigeria vs São Tomé and Príncipe

Israel Adesanya survives Drake curse with victory against Jared Cannonier

Israel Adesanya survives Drake curse with victory against Jared Cannonier

'I have never raised my hand to hit my wife' - Chacha Eke's estranged husband speaks

'I have never raised my hand to hit my wife' - Chacha Eke's estranged husband speaks

Owo massacre: Amotekun arrests suspects in connection with church attack

Owo massacre: Amotekun arrests suspects in connection with church attack

Taiwo Awoniyi set for Union Berlin return just 28 days after joining Nottingham Forest

Taiwo Awoniyi set for Union Berlin return just 28 days after joining Nottingham Forest

N600m Unilorin commercial poultry farm begins operations

N600m Unilorin commercial poultry farm begins operations

Top 5 transfer hijacks in Premier League history

Top 5 transfer hijacks in Premier League history