Pulse.ng logo
Go

Sagir Takai ya fice daga PDP, ya koma jam'iyar PRP

Takai yayi hannun riga da tsohuwar jam'iyar sa wanda a karkashinta ya tsaya takarar gwamna a zaben 2015 bisa rashin adalci da aka nuna masa.

  • Published:
play Sagir Takai ya koma jam'iyar PRP hayan ficewar shi daga PDP (Facebook/rariya)

Dan takarar gwamna a jihar Kano, Salihu Sagir Takai, ya fice daga babban jam'iyar adawa ta PDP bisa rashin adalci da ya fuskanta a cikin jam'iyar.

Takai wanda ya fito takara karkashin PDP a zaben 2015 ya kuma nemi ya zama gwanin jam'iyar a zaben 2019, sai dai hakan bata samu ba inda ya rasa wannan damar ga dan takarar da tsohon Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya amince dashi.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana a makon da ya gabata Abba Kabir Yusuf wanda bangaren Kwankwasiya ke ra'ayi aka tsayar a matsayin dan takarar jam'iyyar ta PDP a Kano, ba Malam Salihu Sagir Takai ba.

Wannan ne kuma dalilin da ya sa Takai ya sauya sheka daga PDP zuwa jam'iyyar PRP.

Takai yana mai cewa "Mun wayi gari a PDP ana yin abin da aka ga dama ba tare da an tafi da 'yan jam'iyya ba,".

Tsohon jigon PDP ya samu kyakkyawar tarba a sabon jam'iyar sa ta PRP kuma alamiu na nuna cewa shi za'a tsayar a matsayin dan takarar gwamna a zaben 2019.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement