Pulse.ng logo
Go

Sadiq Umar Dan wasan Nijeriya ya sauka kasar Scotland domin kammala yarjejeniya na komawa Rangers

Tun ba yau ba sabon kocin kungiyar Rangers ya nuna sha'awar da yake ma dan Nijeriya kuma ya sha alwashin kawo matashin kungiyar.

  • Published:
Nigerian striker Umar Sadiq has arrived Scotland to secure a season-long loan move from Italian Seria A side AS Roma to Scottish Premiership side Rangers. play (SNS Group)

Gwarzon matashin dan kwallon super eagles, Sadiq Umar ya sauka kasar Scotland domin kammala yarjejeniya na komawa kungiyar Rangers da taka leda.

Kamar yadda jaridu suka bayyana, dan wasan zai koma kungiyar ne bisa yarjejeniyar aro daga kungiyar Roma na tsawon shekara daya.

play (SNS Group)

 

Tun ba yau ba sabon kocin kungiyar Rangers ya nuna sha'awar da yake ma dan Nijeriya kuma ya sha alwashin kawo matashin dan kwallon kungiyar.

Tsohon gwarzon dan wasan kungiyar Liverpool yace hazikin matashin yana daya daga cikin dinbim yan wasa da suke birge shi. Ya yaba gwaninta da dan Nijeriyan ke nunawa a filin kwallo.

Dan wasan ya sauka filin jirgin sama ta Edinbugh daidai karfe 10 na safiyar ranar Litinin 9 ga wata domin daukar matakai na karshe kan kwantiragin sa da kungiyar.

A rahoton da jaridar Daily Mail ta fitar, tauraron dan kwallon yana jiran takardar aiki na kasar gabanin sa hannu ga takardar kwantiragi.

play (SNS Group)

 

Sadiq Umar wanda ke taka ma kungiyar As Roma na kasar Italiya wasa zai shiga cikin jerin sabbin yan wasan da sabon kocin Rangers ya kawo.

Kai ga yanzu kungiyar Rangers ta siyo yan wasa bakwai. ga sunayen su kamar haka: Scott Arfield, Allan McGregor, Jamie Murphy, Nikola Katic, Connor Goldson, Ovie Ejaria da Jon Flanagan.

Akwai yiuwar bayan Sadiq Umar shima dan wasan tsakiyar kasar Mali, Lassana Coulibaly, zai dawo kungiyar da taka leda bisa yarjejeniyar aro daga kungiyar Angers na kasar Faransa.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement