Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da ranar talata 11 ga watan Satumba a matsayin ranar hutu domin murnar sabon shekarar musulunci.

Labarin hakan ya fito ne a cikin wata takardar sanarwa da kwamishnan yada labarai Malam Muhammed Garba ya fitar ranar litinin 10 ga wata.

A cikin sanarwa gwamnan jihar Alhaji Abdullahi Umar Ganduje ya taya daukacin al'ummar musulmai murnar shiga watan Muharam wanda ita ce wata na farko.

Gwamnan yayi kira ga al'ummar da su waiwaya su duba ayyukan alheri da suka aikata a cikin shekarar da ya shude kana su yi amfani da wannan damar wajen yi kasar addu'ar zaman lafiya.

Sanarwar ta kuma jaddada wa al'ummar jihar cewa gwamnatin jihar tana bakin kokarin ta wajen inganta walwala a fadin jihar.

Hakazalika sanarwar ta kuma yi kira ga al'ummar jihar da su goyi bayan shugabanci shugaba Muhammadu Buhari domin samad da zaman lafiya da cigaba.

Ranar Talata 11 ga watan Satumba 2018 daukacin musulman duniya zasu yi murnar shiga sabuwar shekarar musulunci ta 1440 bayan hijirar fiyeyen halitta Annabi Muhammad (SAW).