Pulse.ng logo
Go

Ta'adanci Sabuwar hari a jihar Zamfara, mutune da dama sun mutu

Lamarin ya faru ranar alhamis 12 ga wata. Kamar yadda wani shaida ya sanar, mutane da dama sun rasu sakamakon harin da ya faru a filin tonon ma'adanai

  • Published:

Yan ta'adda da suka addabi al'ummar jihar Zamfara sun sake kai hari karamar hukumar Anka, mutane da dama sun rasu sakamakon harin.

A wata labari da NAN ta fitar, maharar sun kai harin kwantar-bauna filin tona ma'adanai dake kauyen Kuru-kuru inda suka sake far ma jama'a kauyen Jarkuka dake makwabtaka da garinĀ  yayin da suke kokarin kaiĀ  dauki ga al'ummar kuru-kuru.

Lamarin ya faru ranar alhamis 12 ga wata. Kamar yadda wani shaida ya sanar, mutane da dama sun rasu sakamakon harin da ya faru a filin tonon ma'adanai.

Shaidar mai suna Sadi Musa, ya kara da cewa, yayin da al'ummar dake makwabtaka da kauyen suka garzaya domin yin jana'izar matattun, mahara suka sake kai hari inda suka kara kashe mutane dama.

Kakakin rundunar yan sanda na jihar DSP Muhammed Shehu ya tabbatar da faruwar hakan. Sai dain bai yi karin haske game da harin inda ya sanar ma manema labarai cewa za'a samu karin haske kan lamarin har sai bayan ya sanar da kwamishnan yan sanda.

Sakamakon hare-haren yan bindiga

Wannan sabuwar hari ya faru bayan sati biyu da kwatancin hari da aka kai kauyen Bawan daji na karamar hukumar Anka wanda yayi sanadiyar mutuwar jama'a da dama.

Duk da albishirin matakin tsawaita tsaro a jihar da shugaban Muhammadu Buhari yayi, jihar Zamfara ta cigaba da fama da hare-haren yan bindiga da barayin shanu.

Sarkin Anka Alhaji Attahiru Ahmad da gwamnan jihar Abdulaziz Yari sun sake kai koken su zauren fadar shugaban kasa kan halin da jihar ke ciki sakamakon harin da aka kai kwanaki kadan bayan ziyarar da shugaban yayi zuwa jihar. Jagororin sun tattauna cikin sirri kan matsalar tsaro da jihar ke fuskanta.

Wannan ya biyo bayan karar da Sarkin ya kai majalisar dinkin duniya inda ya roka a kawo agaji gare su musamman a garin da yake jagoranta.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.