ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamna ya biyo sahun gwamnatin jihar Kaduna wajen tantance malamai

A bisa takarda da kakakin gwamnan Francis Agboh ya fitar ranar laraba, za'a gudanar da jarabawan ga malaman makarantar firamare da na sekandare.

Gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya bayyana kuddirin gabatar da jarabawa domin tantance malamai a jihar.

Gwamna ya sanar da haka a garin Yanagoa babban birnin jihar Bayelsa a wani taro.

A bisa takarda da kakakin gwamnan Francis Agboh ya fitar ranar laraba, za'a gudanar da jarabawan ga malaman makarantar firamare da na sekandare.

Gwamnan yace a zai gabatar da takardar ga yan majalisar dokokin jihar domin su tattauna akai.

ADVERTISEMENT

Kwatankwacin haka ya faru a jihar Kaduna wanda bayan jarabawan gwamnan jihar Malam Nasiru El-rufai ya kori malamai 21,780 sakamakon faduwan da suka yi kan jarabawan da aka yi masu.

Sakamakon korar yasa kungiyar malamai da na kwadago suka gabatar da zanga-zanga domin nuna fushin su game da matakin da gwamnan ya dauka.

Wannan lamarin dai ya kawo cece-kuce a fadin kasar inda dubban mutane na goyon bayan matakin da gwamnan ya dauka wajen inganta fannin ilimi. Hakazalika wasu na ganin cewa matakin yayi tsauri.

Kan batun malaman Kaduna shima shugaban kasa Muhammadu Buhari ya goyi bayan gwamnan wajen inganta fannin ilimi a jihar inda yake la'akari cewa idan an inganta fannin ilimi kasar zata samu cigaba.

ADVERTISEMENT

Bisa ga matakin da gwamnan ya dauka, wasu jihohi sun kwaikwayi hanyar da gwamnatin Kaduna ta dauka wajen gabatar da jarabawa domin tantance ingantattun malamai a jihohin su ciki har da jihar Kogi da Bayelsa.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT