Pulse.ng logo
Go

Da dumi-dumi Sabon rikici ya barke a jihar Filato, mutum 25 sun rasa rayuka

Maza 19, mata 3 da yara 3 suka mutu sakamakon harin da ake zargin wasu makiyaya da kai wa kauyen Dandu dake karamar hukumar Bassa

  • Published:
Zannen jihar Filato a taswirar Nijeriya play

Zannen jihar Filato a taswirar Nijeriya

(Channels tv)

Mun samu labarin sabon rikici da barke a jihar Filato wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum 25.

Ana zargi wasu makiyaya da gudanar da harin wanda yayi sakamakon mutuwar maza 19, mata 3 da yara 3.

Kamar yadda Channelstv ta fitar lamarin ya faru ne a daren ranar litinin 12 ga wata a kauyen Dandu na gundumar Kwall dake karamar hukumar Bassa na jihar.

Wannan lamarin ya faru kwana hudu bayan ziyarar aiki da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai jihar.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement