Filin ƙwallo na Samuel Ogbemudia, wanda yake garin Benin, ya cika da mutane yau domin rantsuwan Gwamnan Edo- Godwin Obaseki. Hukumar ʼƳan Jarida na Najeriya(NAN) sun kawo rahoto cêwa jamaʼa sun cikâ kowane wuri a filin ƙwallo. Mutanen da suka je kalloʼn bikin rantsuwa sune masu fatan alheri, Mataimaka, Abokai da ʼyan uwa.
Manyan mutanen da suka halarta a biki, sune shugaban majalisar Dattijai, Likita Bukola Saraki. Alhaji Aliko Dangote, Gwamna Abdullahi Abubakar na Jihar Bauchi, Gwamna Ibikunle Amosun na Jihar Ogun, da mai takaran Gwanan jihar Ondo akan jamʼiyyar APC- Rotimi Akeredolu.
Sauran baƙin da suka halarta a wannan taro sune Janar Yakubu Gowon (Shugaban Kasar najeriya na da), Ministan Bayanai- Lai Muhammad da sauran ministoci. Obaseki ya yi takaran Gwamnan Jihar Edo akan jamʼiyyar APC a ranar 29 ga watan satumba. Ya lashe zaɓe bayan ya ci ƙaramin hukuma goma sha ukku cikin goma sha takwas. Wani Fasto mai suna Ize-Iyamu ya biyo shi ga baya a cikin zaɓe.