Pulse.ng logo
Go

Ruby Gyang Ta bijire ma bukatar mahaifin ta amma aikin da take yi ya samu karbuwa

Sarauniya Ruby kamar yadda ake mata lakabi ta bayyana mana labarin yadda tayi balaguro daga Jos zuwa Legas domin fafata da sauran mawakan masana'antar.

  • Published:
play (Instagram/rubygyang)

Daya daga cikin matan arewa dake fafatawa a masana'anta nishadi a fanin waka, Ngohide Ruby Ann GyangGyang wacce aka fi sani da Ruby Gyang ta bayyana yadda ta bijire ma bukatar mahaifin ta na zama malamar makaranta zuwa mawakiya.

Haifafiyar 'yar Jos, mawakiyar tana daya daga cikin matan dake tare da shahararren gidan waka, Chocolate city wanda fitaccen mawaki M.I Abaga ke shugabanta.

Hirar mu da ita, Sarauniya Ruby kamar yadda take kiran kanta ta bayyana mana labarin yadda tayi balaguro daga Jos zuwa Legas domin fafata da sauran mawakan masana'antar.

Ruby Gyang tayi karin haske game da rayuwar ta a dandalin waka play

Ruby Gyang

 

Bijire wa mahaifin ta wajen zabar sana'a

Tace tun tana yar shekara 5 take sha'awar yin waka domin kuwa a lokacin tana koyi da fitatun mawakan wannan zamanin irin su Micheal Jackson da sauran su.

Kamar yadda ta bayyana, assali mahaifin ta ya yunkura domin ta zama malamar makarantar kasacewar shi malami ne mai matsayin farfesa, sai daia daga bisani ta bijire masa da taimakon mahaifiyar ta wacce ta goyi bayan ta yayin zabi fannin waka a matsayin aikin da tayi. Ta kara da cewa daga baya mahaifin ta ya amince da sana'ar da ta zaba kuma yayi mata fatan alheri kafin ya rasu.

Kauracewa daga garin Jos zuwa Legas bayan kammala karatu

Game da zamanta a Chocolate city, tace alaka ce wacce suka kulla da su M.I da Jesse Jags tun suna garin Jos domin a gareta kamfanin na yan gida daya ne.

Wakar ta ya sha bamban da na mafi yawancin mawakan yanzu kuma kamar yadda ta bayyana sallon wakar ta yana mai jirgiza zukata tare da farantar da rai.

"irin sallon wakan da nake yi shine 'soul music' na sha bamban da sauran. wato waka wacce take fitowa ba tare da kide-kide da yawa ba kuma mafi yawanci waka ce wanda ake yi don isar da sako mai razanar da zuciya imma soyayya ko halin rayuwa na yau da kullum" Tayi karin haske.

Kalubalen da ta fuskanta a Legas

Mun tambayeta game da kalubalen da ta fuskanta sanda ta koma Legas da zama domin mayar da hankali kan sana'ar ta, ga abun da ta fada;

"A gaskiya M.I ya taimake ni sosai lokacin da ta fara waka dindindin bayan kammala karatuna. lokacin da na shiga masana'antar babu mata da yawa musamman ma matan arewa. Aikin sai yayi mun nauyi ganin yadda za kara da maza amma cikin halin kyautatawa M.I ya zagaya dani wurare da dama domin fitar da wakoki na musamman kafofin watsa labarai da wurin masu hannu da shuni a dandalin nishadantarwa".

Ta nuna farin cikin ta bisa yadda mutane da dama suka karbi wakokin ta da hannu biyu. Tana mai cewa "Tun da na fara mutane da dama sun karbe ni hannu biyu a jihar Legas abun ya kara birgeni sanda na gan yadda mutanen arewa musamnan yan jos suka tarbe ni tare da nuna farin cikin su ga aikin da nike yi. Waka ita kadai ne abun da nake takama dashi , ita kadai na iya kuma jama'a na alfahari dani".

 

Ta kara da cewa a farko ta fara waka ne a cikin harshen turanci zalla amma bayan shawara da aka bata ta fara saka harshen hausa kuma yin haka yayi tasiri sosai.

Tace akwai wakoki da dama da take shirayawa a halin yanzu amma wanda zata fitar nan bada dadewa ba shine wanda ta shirya da mawaki Classiq da Kheengz.

Daga karshe ta jinjina ma sauran mawakan arewa bisa rawar da suke takawa wajen bayyana basirar su ga jama'ar kasa har da na kasashen waje.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.