Har yanzu kura bata lafa ba game da zaben fidda gwani na jamiyar APC a jihar Zamfara, uwar jamiya ta dau mataki na rushe shugabanninta na jihar.

Matakin ya fito ne a cikin wata sanarwa da jam'iyar ta fitar mai dauke da sa hannun kakakin jam'iyar, Yekini Nabena.

Bisa ga wannan sabon matakin duk wani shugabanci na jam'iyar a jihar Zamfara ta rushe.

Sanarwar tace an baiwa kwamitin da aka kaddamar na gudanar da zaben jam'iyar a jihar damar cigaba da aikin zaben fidda gwani na jihar.

Ta kuma gargadi gwamnatin Abdul'aziz Yari da shugabannin jam'iyar da aka rusa da kada su kawo ma kwamitin cikas wajen tafiyar da alamuran zaben tantance wadanda zasu wakilci jam'iyar a zaben 2019 a jihar.

Matakin ya biyo bayan takaddamar da aka yi game da zaben fidda gwani a jihar.

An kuma samu barkewar rikici a jihar bayan nadin da uwar jam'iyyar ta sake yi wa Dakta Abubakar Fari, wato shugaban kwamitin da ya soke zaben fidda gwanin da aka fara a makon da ya gabata a matsayin wanda zai jagoranci sabon kwamitin da zai gudanar da zabe.

Game da wannan sabon mataki da uwar jam'iyar ta dauka, gwamnan Zamfara ya mayar da martani ya ce ba za su yarda da alkalancin shugaban kwamitin zaben ba, kuma ya kalubalanci shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Adams Oshiomole.

A labarin da BBC Hausa ta fitar, gwamna Abdul'aziz Yari, yacce ba za su lamunci aringizon zabe ba, sannan yace shugaban jam'iyyar APC ta kasa ya yi kadan ya ce zai yi iko a jihar Zamfara don haka indai ba za a musu abinda suke so ba to a manta da batun zabe a zamfara.

Kai ga yanzu jihar Zamfara tana daya daga cikin jihohin da ba'a kammala zaben fitar da yan takarar APC. Sai dai kuma ana sa ran cewa yau Asabar jama'a zasu san inda aka dosa game da yan takarar jihohin gabanin zaben 2019.

A gobe Lahadi ne wa'adin kammala zaben fidda gwanin don mika wa hukumar zabe 'yan takarar zai cika.