Dan takarar kujerar shugaban kasar Brazil ya tsallake rijiya ta baya bayan wani hari da aka kai masa yayin da yake kamfe.

Yayin da dan takarar ke gudanar da gangamin yakin neman zabensa a garin Juiz Fora wani mahari ya dabba masa wuka a ciki.

[No available link text]

An garzaya da Jair Bolsonaro wanda ake wa lakabin Donald Trump din Brazil asibiti cikin gaggawa.

Likitoci dake kula dashi sunce yana cikin mummunar hali duk nasarar da aka samu wajen yi masa tiyata.

Mista Bolsonaro shi ne kan gaba a dukkanin kuri'un jin ra'ayin jama'a da aka gudanar gabanin zaben Brazil da za a gudanar a watan gobe.

[No available link text]

Yan sanda sunce sun cafke maharin da ta aikata laifin nan take yayin da yake neman kubuta.

Magoya bayan sunce anyi yunkurin kashe dan takarar su wanda ake ganin shi zai lashe zabe.

Shugaban kasa  Micheal Temer yayi Allha-wadai da lamarin. A cewar shji abu ne wanda ba za taba amince dashi a kasar Brazil wanda take bin tsarin dimokradiya.