Fitaccen jarumin fim kum mawaki Adam A. Zango ya nemi afuwar abokin sanaar sa na dandalin Kannywood Ali Nuhu.

Sakon yana dauke da hoton Zango inda ya durkusa yayin da shi kuma Ali Nuhu yana zaune bisa kujera. Sakan da zango ya rubuta na cewa "tuba nake sarki gwiwowina a kasa".

Hakan dai ya biyo bayan jerin hotunan su tare da Shugaban kamfanin White House Family ya wallafa a shafin sa bayan sun kwashi kwanaki suna gaba.

Alamu na nuna cewa wasu mutane da basa so a zauna lafiya tsakanin fitattun jaruman suke hura wutar gabar.

A sakon da ya wallafa a shafin sa kwanan baya mai dauke da hoton sa da Ali Nuhu, Adam Zango ya rubuta "Karshen munafukai...mai wuri ya dawo...Allah ina godiya da irin wadannan jarabtar da ka yi min"

Wasu masana dai na ganin hassada da girman kai ne ke sanya 'yan wasan na Kannywood biyu ke gaba da juna.

Ga dukanin alamu duk wata gaba dake tsakani su ya gama ci idan aka yi la'akari da sakonin da jaruman ke wallafawa a shafukan su.

Bayan fim dinsa "Mansoor" ya lashe lambar yabo ta gasar AMVCA, Zango ya taya Ali Nuhu murna inda shima 'Sarkin Kannywood' gode masa.