ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Ribar da na samu na zama gwarzon shekara, jarumi ya bayyana cigaban da ya samu gabanin gasar AMMA

Bisa ga darajar da ya samu kamfanin TECNO ta kaddamar dashi a matsayin jakadar ta a Nijeriya

Jarumin wanda ya lashe kyautar bisa rawar da ya taka a shirin "Uwata ce", ya nuna farin cikin samun kyautar a takarar gasar wanda aka hada shi takara da fitattun jarumai.

A karshen makon da ya gabata ne aka shirya taron gasar karrama fitattun mawaka da yan wasan kwaikwayon arewa da suka yi fice a shekara.

Karo na biyar na bikin wanda aka gudanar a garin Katsina ya samu halarcin manyan fuskoki na daga cikin jagororin masana'antar kannywood.

ADVERTISEMENT

Hirar shi da BBC, Isa A.Isa ya bayyana cewa bai taba samun irin wannan gaggarumar kyautar ba a duk tsawon shekaru sama da 20 da yake masana'antar fim.

Bisa ga darajar da ya samu na lashe kyautar gwarzon shekara, kamfanin waya ta TECNO wanda take daya daga cikin kamfanuka da suka dauki nauyin bikin gasar ta kaddamar dashi a matsayin jakadar ta na Nijeriya.

Bugu da kari jarumin yace gabanin darajar da ya samu wasu manyan masu shirya  fim sun garzawa ofishin sa domin ya rattaba hannun ga takarda na fito a wasu fina-finan da suke shirin yi.

Yana mai cewa "Alhamdulillah ni dai a wannan shekarar babu abun da zan ce sai dai godiya".

Yayin da ya zamanto gwarzo, ita kuma jaruma Halima Atete ta zama abokiyar takamar shi inda itama ta lashe kyautar gwarzuwar shekara.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

Here's everything to know about being a virgin on your wedding night

Here's everything to know about being a virgin on your wedding night

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

Top 5 female directors in Nollywood

Top 5 female directors in Nollywood

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 reasons Easter was more fun when we were children

5 reasons Easter was more fun when we were children

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT