Pulse.ng logo
Go

Isyaka Rabiu Rayuwar Khalifa Isyaka Rabiu kafin rasuwar sa

Shahararren malamin kuma hamshakin dan kasuwa, ya rasu a yammacin ranar talata 8 ga wata a birnin London bayan rashin lafiya da ya sha fama da ita

  • Published:
Khalifa Isyaka Rabiu ya rasu yana da shekara 90 a duniya play

Khalifa Isyaka Rabiu ya rasu yana da shekara 90 a duniya

(DailyNigerian)

Labarin rasuwar daya daga cikin manyan malaman addinin na kasa, Khalifa Isyaka Rabiu, yana cigaba da razanar da zukata.

Shahararren malamin kuma hamshakin dan kasuwa, ya rasu a yammacin ranar talata 8 ga wata a birnin London bayan rashin lafiya da ya sha fama da ita.

Kafina rasuwar sa, malamin wanda aka wa lakabin "Khadimul Qur'an" yana rike da mukamin Khalifar darikar Tijjaniya na Nijeriya.

Ga takaitaccen tarihin rayuwar sa kamar haka;

Haifafen dan jihar Kano

An haifi Sheikh Isyaka Rabiu cikin shekarar 1928 a garin Bichi dake nan jihar Kano ga iyalan malam Muhammad Rabiu Dan Tinki.

Daga 1936 zuwa 1942, marigayin ya halarci makarantar allo ta mahaifinsa, inda aka horar da shi kan Alkur'ani da Larabci. Daga nan ya tafi Maiduguri domin karo ilimi.

Malamkatar sa

Bayan ya yi auren kuma ya tafi Zaria gidan wani shahararran Malami, mai suna Malam Na'iya, inda ya samu shekaru biyu yana dalibta.

A shekarar 1949 ya kasance malamin addini mai zaman kansa, inda yake koyar da Larabci da Alkur'ani ga dalibansa.

Harkar Kasuwanci

Duk da cewa yana koyarwa, Sheikh Isyaka Rabiu ya fara kasuwanci cikin shekarar 1950. Kana a cikin shekarar 1952 ya kafa kamfanin sa mai suna Isyaka Rabiu and sons.

Kamfanin ya fara da zama dilan kayan kamfanin UAC ne, wanda a wancan lokacin ke kasuwanci akan kekunan dinki, da litattafan addinin Musulunci da kuma kekuna.

A 1958, kamfanin ya sami bunkasa bayan da aka kafa masakar Kaduna Textile Limited kuma kamfanin na Isyaku Rabiu & Sons ya zama daya daga cikin dilolinsa na farko.

Kamfanin da marigayin ya kafa na Isyaku Rabiu & Sons a matsayin kamfani mai kasuwancin gine-gine da harkar inshora da na banki da kuma saye da sayarwar filaye.

A shekarun 1970, kamfanin ya zuba jari cikin harkar hada akwatuna da jakukkuna, kuma wannan wani hadin gwuiwa ne da wasu masu zuba jari daga Lebanon.

A 1972 ya kafa masakar Bagauda Textile Mill, masu saka zannuwa da kayan inifom, inda daga nan ne ya kafa wasu kamfanonin da ke kasuwanci a bangarori daban-daban na tattalin arzikin kasar.

Wasu daga cikin sassan sun hada da kasuwanci kan kifi, da harkar gidaje da filaye, da siga, da kamfanin da ke samar da kayan motoci musamman na Daihatsu.

Ayyukan raya al'umma

Shaikh Isyaka Rabiu ya kasance abun koyi a cikin al'umma bisa irin gudummawar da yake bayar wa wajen tallafa wa jama'a

Ban da fagen karatun addini da kasuwanci, marigayi Sheikh Isyaku Rabi'u ya yi fice wajen ayyukan taimako, wanda ya sa mutane da dama ke kaunarsa.

Malamin ya rasu yana da shekaru 90 a duniya kuma ya bar mata da yara 42 da jikoki da dama.

Kafin rasuwar sa, shine jagoran mabiyan darikar tijjaniya.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.