ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Mahaifin Sambo Dasuƙi, waton Sarkin Muslumai na da-Ibrahim Dasuki- ya rasu

Hukumar Labarai na Najeriya (NAN) sun yi rahoto cewa wannan Sultan na 18 ya rasu bayan dogon rashin lafiyan.

Mahaifin Sambo Dasuƙi, waton Sarkin Muslumai na da-Ibrahim Dasuki- ya rasu

Ya ce za a binne shi yau a Hubbaren Shehu, Sokoto, bayan Sallah na Zuhr. An ƙara bayani da cewa za a yi Sallah na Janaʼizar sa a Babban Masallaci Jumaʼa na Sarki Muhammadu Bello a wannan rana.

Marigayi Alhaji Ibrahim Dasuƙi shi ne Sarkin Muslumai daga 6 Nuwamba, 1988 zuwa 20 Afrilu 1996. An hambara shi daga kujera a lokacin Mulkin Soja na Marigayi Janar Sani Abacha. Kafin ya zama Sarki, an naɗe Alhaji Ibrahim da rawanin Baraden Sokoto. Dasuƙi shi ne Sarki na Farko daga Gidan Buhari, Jikan Usman Ibn Fodio. Da tasirinsa aka kafa Ƙungiyar Jamaʼatu Nasril Islam. An haife shi a ranar 31, Disamba 1923.

Allah (SWA) ya yi masa gafara. Allah ya yi masa rahama da Al-Jannah Firdaus. Amin

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT