ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Abun daya kamata ka sani game da zakkat-ul-fitr

Wannan zakka ta na wajaba ne a kan 'da, ko bawa namiji ko mace, babba ko yaro, matukar dai musulmi ne wanda ya mallaki abincin wuni daya.

Zakatul Fitr

Idan Azumi ya kai gab da karshe, akwai Zakkar abinci da ake bayarwa don dada samun lada a wurin Allah da kuma kankare zunubban da suka yi saura na miyagun maganganu da makamantansu, shi ya sa ma ake kiranta da sunan "ZAKKAR FIDDA-KAI"

Bayar da wannan Zakkar wajibi (farilla) ne, kamar yadda Hadisin Abdullahi Dan Umar (RA) ya nuna. (Riwayar Bukhari da Muslim).

Kuma ta na wajaba ne a kan ɗa, ko bawa namiji ko mace, babba ko yaro, matukar dai musulmi ne wanda ya mallaki abincin wuni daya, na sa da na iyalansa, ba sai wanda ya

mallaki dukiya mai yawa ba. Abdullahi Dan Umar (RA) kuma cewa ya yi: "Manzon Allah (SAW) yayi umarni da zakkan fidda kai ga yaro da babba, ɗa da bawa, daga wadanda kuke kulawa dasu”

ADVERTISEMENT

Abun da za’a iya bayar

Za a bayar da Sa'i guda ne na kowane mutum daga dukkan nau'in abin da ake kiransa abinci, ba lallai sai dabino ko Sha'ir ko Alkama ba, wannan shi ne bayanin da malamai suka tabbatar.

Don haka za a iya bayar da sa'in dawa, gero, masara, shinkafa da garin hatsi, ko na kwaki, matukar dai abinci ne babu laifi. [Dun karin bayani duba Sifatu Saumin Nabiyyi (SAW) Akwai Malaman da suke ganin in har akwai bukatar a bayar da kima, ko kudi, ana iya bayarwa, amma a bayar da abin da shi ya fi tun da dai tambarin talaka fa cikinsa ne!

Lokacin fitarwa

Ana bayar da wannan Zakkar ne ana gobe sallah kafin a fita zuwa Masallaci, kamar yadda Hadisin 'Dan Umar (RA) ya nuna cewa "Manzon Allah (SAW) yayi umarni da bayar da zakkan fidda kai kafin fitan mutane zuwa masallaci” [Bukhari da Muslim].

ADVERTISEMENT

Amma ya halatta a bayar kwana daya ko biyu kafin sallah, saboda maganan Nafi'u (RA) da ya yi na cewa "Abdullahi dan Umar (RA) ya kasance yana ba da wadanda suke karban (zakkar), sun kasance ana basu ne kafin ranar Eid da kwana daya ko biyu”(Bukhari da Muslim).

Wanda ake ba

Za a bawa miskini ne ko fakiri wanda ba ya da hali, kamar dai yadda Annabi (SAW) ya ambaci lafazin Miskini, to shi ne za a ba shi, ba lallai sai an rarraba ga wadanda aka ambace su a cikin Ayar Zakka ba cikin suratul Taubah, amma wani yana iya hawa tudu biyu, a ba shi don ya cancanta, sannan sai ya bayar don ya samu wadatuwa.

Kuma lallai ne a bayar da zakkar kafin a tafi masallacin Idi, don Annabi (SAW) ya ce: "duk wanda ya bayar kafin aje sallah, zakka ce karbabbiya, wanda ya bayar bayan sallah kuma sadaqa ce daga cikin sadakoki kawai”

Don haka sai a yi kokari a bayar da wuri don a kwantar wa miskinai da hankali, a sanya musu farin ciki da walwala, a kuma rufa mu su asirinsu, don su ji dadin shagulgulan Idi tare da iyalansu da abokansu da 'yan uwansu.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

Here's everything to know about being a virgin on your wedding night

Here's everything to know about being a virgin on your wedding night

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

Top 5 female directors in Nollywood

Top 5 female directors in Nollywood

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 reasons Easter was more fun when we were children

5 reasons Easter was more fun when we were children

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT