ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamnatin tarayya ta ba kasar Saudiya hakuri dangane da rikicin rabon dabino

Ma’aikatar harkokin kasar waje tace tana bincike kan lamarin kuma tana ma gwamnatin saudiya godiya dangane da kyautar da tayi.

Dates

Ma’aikatar harkokin kasar waje tana ba kasar saudiya hakuri dangane da abun kunya da ya faru da kyautar dabino da ta bada don a raba ma yan gudun hijira.

Gwamnatin kasar saudiya ta turo tulin dabino a matsayin kyauta da za’a raba ma masu azumi, amma wasu bata-gari sun amfani da damar don samar ma kansu kudi tunda aka gano cewa ana siyar dashi a kasuwannin dake garin Abuja.

Ma’aikatar harkokin kasar waje tace tana bincike akan lamarin kuma tana ma kasar saudiya godiya bisa ga karamcin.

Ta bakin kakakin ma’aikatar Clement Aduku; “ina so a lura cewa lokacin da dabinon suka kai masaukin karshe, mai’aikatar harkokin kasar waje bata da wata masaniya game da yanda rabon ya kasance.

ADVERTISEMENT

“munji kunya sosai da muka ji labari cewa wasu bata-gari sunyi gaba da dabinon”

“Muna fatan kyakyawar muamala da hadin gwiwa da kasar mu da Saudiya ke dashi zai cigaba”

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT