Tauraron dan wasa, Cristiano Ronaldo ya kafa tarihi a Real Madrid bayan shekara 9 da yi masu hidima.

Dan wasan ya amince da komawa Kungiyar Juventus da taka leda a kakar nan gaba bayan ya taimaki kungiyar wajen lashe kofin zakarun turai na 13.

Ya amince da yarjejeniyar dala miliyan $111 wanda zai kai tsawon shekara hudu yana taka ma kungiyar kwallo.

Labarin ficewar shi daga Real madrid ya mamaye kafafen sada zumunta inda ya zama batun muhawara, wasu na da ra'ayi cewa basu yi tunanin zai koma Juventus.

Dan kasar Portugal kuma jagoran tawagar yan kwallon kasar ya koma Real Madrid cikin shekarar 2009 daga Manchester United dake kasar Ingila.

Ya shigo kasar Spain yana da shekaru 24 kuma ya bar ta yana da shekara 33.

Sakamakon shekarun tara da yayi a kungiyar Real Madrid, tauraron zamani yayi nasarar buga wasanni 438 kuma yayi nasarar zura kwallaye 450 a raga wanda dashi yake rike da matsayin dan kwallo mafi kwallo a tarihin gasar la liga har ma da tarihin kungiyar Madrid.

Sauran nasarorin da ya samu sun hada da; kofin zakarun Spain ta La liga 2.

Kofin copa del rey 2, kofin zakarun turai 4, kofin Uefa super cup 2, kofin gasar duniya da kungiya-kungiya 3 da Supercopa 2.

Bugu da kari jarumin yayi nasara zama zakaran yan wasan kwallo na duniya sau 4 ( hada da wanda ya samu a tsohon kungiyar sa sau biyar kenan).

Kungiyar real madrid tare da dinbim masoyan sa na kungiyar suna kewar sa ganin yadda ya taka rawar gani a kungiyar. Wasu da dama sunyi masa fatan alheri a sabon kungiyar da ya koma.

A halin yanxu dai madrid na neman wanda zai maye gurbin sa.

Rahotanni sun nuna cewa kungiyar tana neman kawo Eden Hazard ko Neymar ko Kylian Mbappe domin maye gurbin sa a tawagar yan wasan gaban ta.