Jiga-jigan yan siyasar nijeriya da masu rike da muhinmman mukami a fadin kasar sunyi jimamin mutuwar tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya, Adamu Ciroma.

Malam Adamu Ciromaya rasu ranar alhamis 5 ga watan Yuli a asibitin Turkish Nizamiye  dake nan garin Abuja bayan rashin lafiya da ya fama da ita.

Shugaban kasa da sauran yan siyasa sunyi jimamin mutuwar sa

Shugaba Muhammadu Buhari a cikin wata sakon ta'aziya da ya fitar, shugaban yace kasar baza ta manta da irin gudumawar da tsohon ministan yayi.

Shugaban yace kasar zata karrama shi bisa taimakon da yayi wajen gina dimokrdaiya a kasar kuma tarihin sa zai zama abun koyi ga sauran yan siyasa dake da manufar yi ma al'umma hidima.

Daga karshe yayi ma marigayin addu'a tare da baiwa iyalen da ya bari fatan samun hakurin jure rashin da suka samu.

Shima shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, a wata sako da ya wallafa a shafin sa na Twitter ya kira marigayin a matsayin wanda yayi kasa hidima mara iyaka. Yace mutuwar sa babban rashi ne ga Nijeriya.

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace daga cikin abubuwan da suka taimake shi a rayuwa shine tunatarwa da shawarwari da ya samu daga mariagayin sanda yake .

Atiku yace tsohon ministan ya bar tarihi a harkar siyasa da shugabanci.

Anyi sallar jana'izar marigayi a Abuja

[No available link text]

Anyi jana'izar shi a nan masallacin birnin tarayya yammacin ranar alhamis. Manyan masu hanu da shuni a harkar siyasa sun halarci jana'izar sa cikin su akwa shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da gwamnan jihar Yobe da Kebbi tare da Sarkin garin Fika dake jihar Yobe.

Shima shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Alhaji Abba Kyari ya halarci jana'izar marigayin.

Malam Adamu Ciroma shine a gwamnan bankin tarayya tsakanin watan Satumba na 1975 zuwa Yuni na 1977.

Haifafen dan jihar Yobe ya rike matsayin ministan Kudi da minisatan noma a karkashin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo. Bayan haka ya kuma rike mukamin ministan noma.

Yana daya daga cikin kashin bayan da suka gina jam'iyar PDP kuma shine shugaban yakin neman zaben Obasanjo gabanin zaben 2003.

Mutuwar sa ya girgaza zukata da dama duba da gudunmawar da ya bayar wajen harkokin siyasa da kuma raya kasar.