Dan takarar shugaban kasa karkashin jamiyar PDP, Atiku Abubakar, ya zabi tsohon gwamnan jihar Anambra a matsayin abokin takarar sa na zaben 2019.

A halin yanzu jiga-jigan suna cikin ganawa ta sirri a nan garin Abuja. Wani shaida dake wajen ganawar tasu ya shaida ma Pulse cewa Peter shine wanda zai mara ma Atiku baya.

Muna sa ran cewa za'a fitar da sanarwa game da zabin nan bada dadewa ba.