Pulse.ng logo
Go

Neman zarcewan Buhari PDP bata fargaba kan wa'adin shugaba Buhari na tsayawa takara

Shehu Yusuf ya shaida cewa PDP zata kwace mulki daga hannun APC a zaben 2019 ganin yadda talakawa ke fama da kuncin rayuwa a karkashin mulkin ta

  • Published:
Many reportedly injured as APC, PDP members clash play

Flags of the People's Democratic Party (PDP)

(NigerianEye)

Jam'iyar adawa PDP tayi fashin baki kan matakin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dauka na neman zarcewa a kan mulki.

Duk da cewa uwar jam'iyar ta sanar cewa zata mayar da martani kan matakin da shugaban ya dauka idan har jam'iyar APC ta bashi tikitin neman zabe, wani jigon jam'iyar ya bayyana cewa kuddurin shugaban ba abun fargaba bace a wajen su.

A wata labari da BBC ta fitar, mai magana da yawun shugaban jam'iyar PDP Shehu Yusuf ya shaida cewa PDP zata kwace mulki daga hannun APC a zaben 2019 ganin yadda talakawa ke fama da kuncin rayuwa a karkashin mulkin ta.

Bayan watanni da jiran tsammani, shugaba Buhari ya sanar da anniyar sa na neman zarcewa kan mulkin kasa a zaben shekara mai zuwa.

Shugaban ya sanar da haka ne a taron shugaban jam'iyar mai ci da aka gudanar ranar litinin 9 ga watan Afrilu. Yace babban dalilin da ya sanya zai nemi zarcewa shine ganin yadda jama'a da dama suka bukaci shi da ya nemi zarcewa.

A wata sanarwa da hadimin shugaban kan harkokin watsa labarai Garba Shehu ya fitar, ya sanar cewa shugaban ya bayyana anniyar sa da wuri domin hukumar zabe ta san matsayin shi kan zabe dake gabatowa.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.