ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Riƙici da yaƙi ba zai kaimu ko ina ba - muƙaddashin shugaban kasa

Osinbajo ya shawarci yan naijeriya dasu ƙauraci maganganu mai tayar da riƙici don shi ke haifar da yaƙi.

Prof Yemi Osinbajo

Muƙaddashin shugaban kasa prof Yemi Osinbajo yace tashin hankali da rigima bata haifar da komai illa yaƙi.

“Abu daya dake bayyane, riƙici bata maganin komai in banda ci baya.

yana da saukin farawa amma wuyan karewa.” ya fada lokacin da yaƙe ganawa da shugabannin yankin kudencin naijeriya.

Ya cigaba da cewa “haƙika a tarihi musamman na zamani, riƙici nada wuyan karewa. Cigaba kawai yake yi. Kuna sane da karin magana na iyamurai wanda tace “duk wanda ƙe gaggawan zuwa yaki, baya ganewa cewar yakin na iya zama mai ajalin sa.”

ADVERTISEMENT

“Mun san mai riƙici ke haifarwa. Nasan ba wanda zaiyi fata koda ma maƙiyin shine da yayi shaidar ganin rikici koda a television.”

“Hakika ba lalle bane riƙici ya fara da makami, yawanci magana ke haifarwa. Zagi da maganganun bacin rai. Shiyasa aka ce harshe yafi takobi matsayi, don shi harshe ke samo ma takobi aiki. Muyi hankali da maganganun dake fitowa daga harshen mu.” yace.

Osinbajo ya shawarci yan naijeriya dasu dinga jurewa da maganganun batanci, don shi ke haifar da rigima.

Ya kara da  cewa; “a jiya na bayyana a fili cewa maganganun bacin rai, ko na rabuwa, ko nuna hali kwatankwacin haka indai ya saba ma sharia, zamu dauki mataki mai tsanani akan shi na doka. Kuma ina kara fadi a yau cewa babu shakka gwamnati baza ta yi shuru dangane da duk wani magana da zai kawo bacin rai ko na rabuwa.”

“Zamu dauki mataki mai tsanani ma duk wani magana wanda haifar da rikici ko mai rushe zaman lafiya a naijeriya, gaskiya baza mu yarda ba. Dalilin da ya sa baza mu yarda ba shine, don wadanda basu da laifi akan haka suna bukatar kariya da tsaro. Kuma ina mai tunani cewa a matsayin mu na gwmnati hakki ne a gare mu na kare yan naijeriya da duk wanda ke cikin kasar.”

ADVERTISEMENT

“Hakkin gwamnati ne na samun hanyar tabbatar da wannan manufar. Akwai wata magana da shugaban Buhari ke yawan fadi kuma ina zato kuna jinshi yana fadi, yana cewa; “ in babu zaman lafiya da tsaro babu yanda za’a samu cigaba. Farkon abun da ya zama wajibi gare mu don mu samu cigaba shine mu tabbatar da zaman lafiya da tsaro. Babu yanda za’a samu cigaba a kasa in babu zaman lafiya da tsaro tsakanin al’umma dake cikin ta.”

“Dalilin haka zamu ɗauki mataki na gaske kuma zamu ɗauki nauyin yin haka. Wasu daga cikin nauyin ya kunshi jin kukan ku, shawarar ku da duk wani taimako da zaku iya bada wa don ko wani dan kasa yasan muhimmancin shi a kasar. Shiyasa muka taru anan yau. Ina sa rai cewa ganawar mu zai wayar da idon mu na ganin cewa kasar mu mai albarka ne kuma na zaman lafiya.

Wannan lokacin nada muhimmanci a gare mu da kasar baki daya, kuma ina sa rai cewa a karshe zamu gamsu da cewa mun cinma wani buri dan kanmu da rayuwar nan gaba. Da yardar Allah zamu rayu har mu gan zaman lafiya, tsaro da cigaba na bunkasa a cikin kasa. Kasar da duk da banbancin al’adu, addini, jinsi da shekaru zata zauna cikin lumana.”

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT