ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Mukaddashin shugaban kasa ya bukaci a karfafa tsaro a jihar Kaduna

Osinbajo yace gwamnatin tarayya ta damu inda ya yi inƙari cewa rashin tsaro ya haddasa rikici a yankin kudancin jihar wanda yayi sandiyar rasa rayuka

Acting President Yemi Osinbajo

Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya bukaci a karfafa tsaro a jihar Kaduna kan riƙicin da ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama da ya faru a karamar huƙumar Kajuru na jihar.

A wani bayani da kakakin mukaddashin Laolu Akande ya fitar, Osinbajo ya nuna damuwa game da riƙicin da ya faru

Mukaddashin yace za’a ɗau matakai na kama wadanda suka haddasa riƙicin don shari’a ta hukunta su.

A bayanin shi rashin tsaro a yankin kudancin kaduna abun damuwa ne ga gwamnatin tarayya da ma sauran jama’ar kasa.

ADVERTISEMENT

A karshe Osinbajo ya jajanta ma dangin wadanda rikicin ya shafa, gwamnatin jihar Kaduna da al’ummar jihar kuma yana ma wadanda suka ji rauni fatan samun saiuki cikin gaggawa.

Akalla mutum 36 suka mutu yayin da wasu da dama suka ji rauni sanadiyar riƙicin kabilanci da ya faru a karamar hukumar Kajuru wanda ya faru tsakanin ranar 15 da 17 na watan Yuli.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT