Shugaban jamiyar APC, Adams Oshiomole, yayi tsokaci game da matakin da hukumar zabe ta INEC ta dauka na hana jamiyar fitar da yan takara a jihar Zamfara.

Hukumar zabe ta dauki mataki na sauke yan takarar APC na jihar duba da goyon bayan kundin tsarin dokar zabe.

A cikin wani sako da kakakin hukumar ya fitar  ma jam'iya mai mulki, hukumar tayi duba da sashi 87 da 31 na kundin zabe wajen daukar wannan matakin.

Jagoran jam'iyar APC yace yakamata INEC ta tuhumi jam'iyar gabanin daukar matakin hana ta fitar da yan takara.

Shugaban ya mayar da martani kan batun ta hanyar wasika da ya tura ma sakataren INEC, Okechukwu Ndeche.

Ya ce a jadawalin zabe da hukumar INEC ta fitar, ya bai wa jam'iyyu zuwa ranar 18 ga watan Oktobar 2018 ta aika da sunayen 'yan takararta.

Ya ce a matsayinsu na jam'iyya suna bin duka hanyoyin da suke da su wajen ganin su fitar da gwanayen da za su tsaya takarar gwamna da 'yan majalisun jiha da na dokoki a jihar Zamfara.

Takaddamar yan takarar APC a jihar Zamfara

Rikici ya barke tsakanin yan takarar APC a jihar inda tawagar gwamnan jihar da daya daga cikin yan takarar gwamna, Sanata Kabir Marafa, suka samu rashin jituwa.

APC na jihar Zamafara sun samu baraka ne yayin da gwamna Abdul'aziz Yari ya nemi dan takarar da ya fitar ya zama wanda zai zama dan takarar APC na kujerar gwamna amma sauran yan takarar jam'iyar basu amince da hakan ba.

Sau da dama aka soke zaben fidda gwani ta kwamitin zabe da uwar jam'iyar ta tura jihar domin gabatar da zaben fitar da gwanaye.

Takaddamar jam'iyar a jihar ya kai ga matakin rushe shugabanin APC na jihar.