Rahotanni daga garin Abeokuta na tabbatar da cewa tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo, na shirin mara ma Atiku Abubakar baya a zaben 2019 domin kayar da shugaba Buhari.

Labarin haka ya fito ne yayin da dan takarar shugaban kasa  na PDP ya kai ma tsohon jagoran Nijeriya ziyara a gidansa dake babban birnin jihar Ogun ranar alhamis 11 ga watan Oktoba.

Cikin tawagar da suka garzaya gidan tsohon shugaban kasa akwai shugaban jam'iyar PDP, Uche Secondus, jagoran kungiyar Afenifere, cif Ayo Adebanjo, shugaban yakin neman zaben Atiku, Gbenga Daniel da Sanata Ben Murray-Bruce.

A bangaren malamai kuwa akwai Bishop Mathew Kukah, Bishop David Oyedepo da kuma Sheikh Ahmad Gummi.

Wani majiya ya shaida mana cewa ganawar da jiga-jigan suka yi zata kulla kyakkyawar alaka tsakanin tsofafin abokan hammaya kuma ana kyautata zato cewa Obasanjo zai bude kofar sa na mara ma Atiku baya a zaben 2019 domin kayar anniyar shugaba Buhari na zarcewa a saman kujerar mulkin Nijeriya.

"Ina mai tabbatarwa cewa Kofar Obasanjo a bude take domin mara ma Atiku baya domin kayar da Buhari a zaben 2019" majiyan ya shaida mana.

Wani majiyan da ya halarcin tattaunawar jiga-jigan ya shaida mana cewa anji inda Obasanjo ke cewa "Bari na taya shugaba mai jiran gado, Atiku Abubakar, murna na samun tikitin PDP".