Gwamnan ya ce, idan kowa zai zargi shugabannin coci, bai dace a ce daga dattijon ba.
'OBJ ne Mahaifin cin hanci da rashawa,' Fayose Ya zargi tsohon shugaban ƙasa
Fayose ya ce Obasanjo na ci da barci da cin hanci da rashawa, ya ƙara cewa, gwamnatin sa ta kasance mafi cin hanci da rashawa a tarihin Najeriya.
Ya ce: "Obasanjo da na sani ba shi da kyawawan ɗabi'u kuma ba ya da damar zargin kowa da cin hanci da rashawa, saboda ya na ci da barci da cin hanci da rashawa.
"Idan dole ne kowa zai zargi coci a Najeriya da tallafa cin hanci da rashawa, wannan mutumin ba zai iya zama Obasanjo ba ,saboda ya shugabantar da gwamnati mafi cin hanci da rashawa a tarihin Najeriya.
"Ina Obasanjo ya samu dũkiyar da yake nunawa, tun da shi talaka ne kafin ya zama shugaban ƙasa?
A ina ya sami tiriliyoyin Naira da ya aika a lokacin da ya yi ƙoƙarin ƙara hawan mulki na uku? Ta yaya Obasanjo, wanda a ƙarƙashin zangonsa Najeriya ta shaida faruwar badakalar Halliburton zai yi wa'azi game da cin hanci da rashawa? Wa ya gabatad da siyasa na jakar Ghana-must-go ga majalisar ƙasa?
"Wanene shugaba lokacin da aka nuna buhuna na kuɗi a ƙasa a gidan waƙilai, na cin hanci da aka ba wa wasu mambobin waƙilai don tsige kakaki na da, Ghali N'abba?
"A ƙarƙashin wane gwamnati aka gabatad da shiri na fitar kotu a cikin rigimar toshe biliyan $1,09 na man Malabu a 2006?"
Fayose ya ƙara cewa a ƙarƙashin jagorancin Obasanjo a matsayin shugaban ƙasa, aka sa gwamnoni gudunmawar miliyan N10 don ginin library.
A ranar Asabar, 8 ga watan Afrilu, yayin da yake magana a 2017 a jawabi na Victory Life Bible Church International a Abeokuta Jihar Ogun, Obasanjo ya zargi shugabannin coci da ƙarbar kyaututtuka ba tare da tambayar asalin su ba.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng