ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Gwamnatin tarayya zata bayyana adadin albashin da aka tsayar - inji shugaban kungiyar yan kwadago

A cewar shi fadar shugaban kasa zata sanar da haka bayan ta tattauna kan batun a zaman majalisar koli da zata yi.

NLC President, Mr. Ayuba Wabba

Kungiyar ta cinma matsaya game da batun albashin a rahoton da kwamitinta ta mika ma shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban kungiyar ya bayyana hakan ne yayin da ya tattauna da manema labarai a garin Abuja ranar Litinin 8 ga watan Oktoba.

“Ina mai tabbatar wa ma’aikatan Nijeriya cewar an kamala duk wani shiri kan batun Karin albashi, yanzu haka an mika rahoto kuma za a saka masa hannu cikin wannan satin" inji shugaban kungiyar.

ADVERTISEMENT

Ya milka godiyar sa ga sauran kungiyoyin ma'aikata na kasar da suka amince da biyan albashin da aka tsayar.

Sai dai bai bayyana adadin kudin da kwamitin kungiyar ta tsayar.

Tafiya yajin aiki

Idan ba'a manta ba a makon da ya gabata ne kungiyoyin kwadago na kasa zuka janye yajin aiki da suka tafi bayan da suka cinma matsaya da gwamnati.

Kungiyoyin sun dauki matakin ne domin nuna bacin ransu game da batun albashi mafi karanci na ma'aikata dake kasar wanda gwamnatin tarayya ta kaddamar amma bata fara aiwatar da tsarin ba.

ADVERTISEMENT

NLC tace an dauki matakin zuwa yajin aikin ne bayan wa'adin da suka baiwa gwamnatin tarayya na tsawon kwana 14 domin duba lamarin albashi mafi karanci.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT