ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Ma'aikatan Nijeriya zasu tafi yajin aiki

NLC tace an dauki matakin zuwa yajin aikin ne bayan wa'adin da suka baiwa gwamnatin tarayya na tsawon kwana 14 domin duba lamarin albashi mafi karanci.

'yan kungiyar kwadago yayin da suke gudanar da gangami

Gamayyar Kungiyar NLC da TUC sun kudura anniyar su na tafiya yajin aiki kamar yadda shiugabannin kungiyoyin suka bayyana.

Kungiyoyin sun dauki matakin ne domin nuna bacin ransu game da batun albashi mafi karanci na ma'aikata dake kasar wanda gwamnatin tarayya ta kaddamar amma bata fara aiwatar da tsarin ba.

Labarin tafiya yajin aiki ya fito ne a cikin wata sanarwa da sakataren NLC, Peter Ozo-Eson, ya sa hannu.

ADVERTISEMENT

Sanarwar ta gargadi sauran ya'yan kungiyar dake jihohin kasar da su bada hadin kai wajen bin umarnin uwar kungiyar na tafiya yajin aiki.

Sai dai yajin aikin zai cigaba har zuwa lokacin da aka fitar da sabon umarni kan batun.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT