Kungiyar kwadago ta NLC ta gudanar da zanga-zangan ta baci ofishin kamfanin sadarwa ta MTN dake fadin kasa.

Kungiyar tayi gangamin a jihohin Bauchi, Oyo, Enugu, Kano da Legas domin jawo hankalin kamfanin wajen daidaita lamuran ma'aikatan ta.

Jagoran tawagar yan zanga-zanga a jihar Bauchi, Kwamrade Hashimu Gital, ya zargi kamfanin MTN da rawaita sabonta yarjejeniyar kwantiragi na ma'aikatar a madadin mayar dasu ma'aikata na dindindin domin kaurace ma biyan kudin giratuti da fansho.

Yace kamar yadda sanarwa ta iso masu daga hedkwatar NLC dake Abuja, kungiyar ta ba kamfanin MTN wa'adin kwana uku domin gyara lamuran kyautata ma ma'aikatar ta.

Gital yace ma'aikata dake aiki a kamfanin sun koma tamkar bayi don haka suka daga babbar murya domin tuna ma kamfanin ka'idoji da doka da kungiyar NLC ta kafa domin kwato ma yan kwadago hakkin su.

Martanin kamfanin MTN game da zanga-zangar

A wata takardar sanarwa da ofishin yadda labarai na kamfanin ta fitar, kamfanin ta zargi kungiyar NLC da lalata dukiyoyi.

Sanarwar tace masu zanga-zanga sun far ma harbar ofishin kamfanin dake nan Ikoyi a jihar Legas safiyar ranar litinin 9 ga wata.

Kamar yadda jami'in hulda da jama'a na kamfanin, Mista Tobechukwu Okigbo ya bayyana, MTN tayi Allah wadai game da gangamin da NLC tayi wanda yayi sanadiyar raunata ma'aikata da dama.

Kamfanin tace zata cigaba iya bakin kokarin ta wajen baiwa ma'aikata hakkokin su domin kare martabar ta ba tare da shiga hakkin kowa ba.

Daga karshe MTN tace ta baiwa ko wani ma'aikatar ta damar shiga kungiya muddin hakan ba zai hana su bioyan bukatun jama'a da suke mu'amala dasu.