Ni ba dan siyasa bane kuma ba mawakin siyasa bane - Adam Zango

Adam Zango yace duk wanda ya tsargu da zabin sa dashi yake.

___8880820___2018___9___20___16___adam_a_zango_41431047_706481136352460_4034495878027891798_n

Jarumin wanda ke cikin fitattun jaruman masana'antar Kannywood dake goyon bayan zarcewar shugaba Muhammadu Buhari yace yana baiwa duk wanda yake so gudunmawa ta hanyar sana'ar sa.

Ya bayyana haka ne ta hanyar sako da ya wallafa a shafin sa na Instagram.

Ya rubuta "Ni ba dan siyasa bane kuma ba mawakin siyasa bane sai dai ina baiwa wanda nake so gudun mawa ta hanyar sana'a ta!! Bana cin tuwo da yan wawa."

Ya kara da cewa "Duk wanda ya tsargu dashi nake yi," tare da nuna alama cewa Buhari da El-rufai kadai zai mara wa baya a zaben 2019.

Ko a kwanan baya Zango ya jaddada cewa baya baya siyasa don kudi kuma yana goyon bayan zarcewar Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-rufai domin sune zabin sa kuma zai cigaba da goyon bayan anniyar su gabanin zaben 2019.

Gwarzon jarumin yana cikin fitattun jaruman da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta karrama bayan kaddamar da sabuwar kudin makar yakin neman zaben Buhari mai taken "Sakamakon canji" a cikin watan Nuwamba.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

Bisola Aiyeola opens up on pausing music for Nollywood

Ada Jesus drama: Actress Rita Edochie curses critics on Instagram

Kanye West responds to Kim Kardashian's divorce petition

Avocado Pear: The health benefits of this fruit are priceless

Ngozi Okonjo-Iweala wants us to wear Ankara; here are 4 style tips

The full details behind Rita Edochie, Prophet Odumeje and Ada Jesus' drama

Actress Rachel Bakam is dead

Belly Fat: 5 natural remedies to help you get rid of it

Google honours Oliver De Coque on his 74th posthoumous birthday