ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Hukumar NFF ta hukunta Kocin super Eagles da aka kama yana karban cin hanci

An kama kocin yana karban na-goro daga wasu yan jarida da suka saje tamkar wakilan yan kwallo domin ya saka yan wasan su cikin tawagar yan wasan Nijeriya da zasu taka leda a gasar CHAN 2018.

An kama kocin yana karban na-goro daga wasu yan jarida da suka saje tamkar wakilan yan kwallo domin ya saka yan wasan su cikin tawagar yan wasan Nijeriya da zasu taka leda a gasar CHAN 2018.

Wani kwamitin na musamman da hukumar NFF ta kafa domin bincike kan lamarin ta kama shi da aikata laifin kuma hukumar ta dakatar dashi na tsawon shekara daya tare da cin shi tara na dala dubu biyar ($5,000).

Hukuncin haka ya fito ne a ranar talata 4 ga watan Satumba yayin da kwamitin ta gana da manema labarai a shelkwatar hukumar.

ADVERTISEMENT

Kwamitin wanda Nuhu Ribadu tace kocin ya saba ma ka'idar hukumar kwallo ta FIFA da na NFF.

Sakamakon binciken da wakilin BBC yayi

A cikin bincike da yake yi cikin sirri wakilin BBC dake Ghana Anas Armeyaw tare da taimakon wasu abokan aikinsa suka tunkari kocin inda suka saje kamar wakilan yan kwallo domin tattauna da jagoran yan wasan kan yadda ake zaban dan wasa a cikin tawagar wadanda zasu wakilci kasa.

Bayan kammala tattaunawar su an gan inda yan jaridar suka mika masa kudi dala dubu daya ($1000) da kuddurin kara masa muddin an saka yan wasan su cikin tawagar yan wasan Nijeriya.

Game da lamarin tsohon kocin kungiyar Kano Pillars ya musanta zargin da ake masa na karban cin hanci domin saka sunaye yan wasan.

ADVERTISEMENT

Yace ba shi ya bukaci kudin da yan jaridan suka bashi, haka nan suka bashi tamkar kyauta. Jagoran yana mai yakini cewa bai saba ma ka'idar FIFA ko NFF.

Kwamitin ta bashi damar daukaka karar hukuncin da aka zartar a kanshi ga kwamitin daukaka kara na hukumar NFF.

Lamarin ya faru ne a Ghana yayin gasar kwallo na kasashen yammacin Afrika da aka gudanar a kasar cikin 2017 inda Nijeriya ta zo na biyu bayan Ghana ta doke ta 4-1 a wasan karshe.

Yana daya daga cikin jagororin da ake girmamawa

Salisu Yusuf yana daya daga cikin manyan jagororin yan wasa da ake mutunta a farfajiyar kwallon kafan Nijeriya.

ADVERTISEMENT

Yayi aiki a matsayin mataimakin ga tsofafin jagororin super eagles kama daga Samson Siasia, Sunday Oliseh kai ga Stephen Keshi.

Hakazalika shine mataimakin Gehnot Rohr bayan yan wasan gida da yake jagoranta.

Ya Jagorancin yan wasan U-23 kana ana kyautata zato shi zai jagoranci yan wasan Nijeriya zuwa gasar Olympics a shekarar 2020.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT