Wani mai zaman kashe wando ya samu hanyar samun kudi inda yake amfani da damar lalacewar hanyoyin garin Aba inda yake safarar mutane cikin farashi mai rahusa.
Ga yanda wani ke neman kudin da zai ci da iyalin sa
Wani mazaunin garin Aba Abia ya samun sabuwar hanyar samun kudi inda yake safara da mutane cikin amalanke a farashi mai rahusa kasancewa hanyoyin sun lalace
Recommended articles
Wani dan jarida dake aiki da Imo city News ya gano shi yayin da yake safara da mutane cikin amalanke kuma yana karban naira 20 daga hannun su.
Mutumin wanda yaki bayyana sunan shi, yace ya koma da taimakon mutane ta hanyar safarar da yake yi kuma yana karban yan kwabai daga gare su kasancewa gwamnatin jihar ta kasa gyaran hanyar har ma da na wasu wurare dake jihar.
Yace ya kan samu naira dubu biyu (N2000) a ko wani rana kuma dashi yake ciyar da iyalin shi.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng