ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Rundunar yan tsaro da bincike sun far wa gidan tsohon shugaban kasa

An samu labari cewa rundunar sunyi bincike a gidan kusan sa’o’i 2 tare da kulle hanyoyi dake kusa da gidan.

Former Vice President Namadi Sambo

Jiya 28 ga watan Yuni 2017 rundunar yan tsaro da bincike  sun far wa gidan tsohon shugaban kasa Namadi  Sambo dake no.1 Alimi road na kaduna don yin bincike.

Rundunar sun hada da yan sanda da yan sandan farin kaya tare da jagorancin jami’an hukuma mai yaki da laifuffukan cin hanci da rashawa watau ICPC.

An samu labari cewa rundunar sun kaddamar da bincike har sa’o’i 2  tare da kulle duk wani hanya dake kusa da gidan.

An ruwaito cewa rundunar sun gudanar da binciken don gano wasu takardu da kudi wadda ma suka dauki wani mai aikin hannu da ya taimaka masu wajen bude rufin gidan.

ADVERTISEMENT

Jaridar punch sun ruwaito cewa wannan shine karo na biyar da ake yin bincike a gidan cikin wata 3

Mataimakin Sambo kan watsa labarai, Mallam Umar Sani yace rundunar basu gano komai a binciken da suka yi.

Hukumar yaki da rashawa (EFCC) na gudanar da bincike kan tsohon mataimakin shugaban kasa bisa ga zargin raba wasu kudi kafin a gabatar da zaben shugaban kasa a shekara 2015.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT