ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Yadda gwamnatin Buhari ya kashe kudin sata da aka gano

Buhari ya kara da cewa an samad da 7,001 megawatt na wuta cikin 2017 kuma manufar shi shine a samu 10,000 kafin 2020

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace cikin kudin gwamnati da aka gano daga hannun wasu barayin gwamnatin anyi amfani da wasu cikin kasafin kudi na 2017.

Shugaban ya bayyanar da yadda aka kashe kudaden a wani taro da aka gudanar a garin Abuja ranar talata wanda babban mai kula da harkan kudade na ƙasa Alhaji Idris Ahmed ya wakilce shi.

Tun ba yau ba yan Nijeriya ke neman hanyoyin da aka kashe kudade da hukumar EFCC ta gano daga barayin gwamnati.

Buhari yana cewa,  “ gwamnati na tana iya bakin kokarinta wajen bunkasa harkan kasuwanci a kasa. Cikin kudin da aka gano daga barayin gwamnati anyi amfani dashi cikin kasafin kudi na 2017.”

ADVERTISEMENT

Buhari ya kara da cewa an samad da 7,001 megawatt na wuta cikin 2017 kuma manufar shi shine a samu 10,000MW kafin 2020.

Shugaban yace tsarin asusun gwamnati na ajiyar kudin gwamnati a asusu guda ya taimaka sosai wajen tabbatar da adalci da lura da yadda ake kashe kudade.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT