Pulse.ng logo
Go

Muhammadu Buhari Abubuwa 7 da suka faru yayin da shugaba Buhari ya ziyarci yankin kudancin kasar

Wannan shine karona farko da shugaban ya ziyarci yankin tunda ya hau kujerar mulkin kasa.

  • Published:
Buhari ya amshi sarautu a yankin play

Buhari ya amshi sarautu a yankin

Abubuwa 7 da suka faru yayin da shugaba ya ziyarci yankin kudancin kasar.

Shugaban yana yankin kudancinnkasar inda ya kai ziyarar aiki ga jihar Anambra da Ebonyi.

Wannan shine karona farko da shugaban ya ziyarci yankin tunda ya hau kujerar mulkin kasa.

 

Ga abubuwa bakwai da suka aiku yayin da ya ziyarci yankin:

1. Dai dai karfe 10:30 na safe jirgin shugaban ya sauka a filin jirgin Akanu Abiam dake nan jihar Enugu.

Daga nan shi da tawagar gwamanoni da sarakunan gargajiya na yankin suka kaddamar da tafiyar hanya zuwa garin Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi.

2. Gwamnonin da suka tarbe shi a filin jirgin Akanu Abiam sun hada da na jihar Imo,Enugu, Ebonyi, Abia, da Kogi.

 

3. Jim kadan bayan isowar sa Abakaliki shugaban ya kaddamar da wasu ayyuka ciki har da gada wanda ke babbab titi mahadin jihar Enugu da kasar Kamaru.

 

4. Shugaba Buhari yace zuwan sa yankin ayyah ce mai nuna cewa yana alfahari da al'adu iri-iri dake fadin kasar.

5. shugaban yace al'ummar yankin sun kwantar da hankalin su domin kasafin kudin 2018 zai tallafa masu wajen gabatar da wasu ayyukan cigaba. Cikin ayyukan da za'a gabatar akwai gina gadar 2nd Niger Bridge.

 

6. Shugaban ya samu sarauta a yankin ganin irin rawan da yake takawa na shugabancin kasar. Sarautar da ya amsa sune: Enyioma 1 of Ebonyi (wato Abokin amana na jihar Ebonyi) da Ochioha Ndi Igbo 1 (jagoran yan kabilar ibo).

 

Idan muka waiwaya baya a lokacin kamfe na zaben 2015, Buhari ya samu lakanin 'Okechukwu' yayin da yaje kamfe a yankin.

 

7.  Tsohon gwamnan jihar Ebonyi Sam Egwu ya jinjina wa shugaban game da diyyar biyan wadanda rikicin biyafra ya shafa tare da biyan fanshi ga jami'an tsaro da suka sauya zuwa kasar biyafra a yakin basasa.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement