ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Dan wasa ya iso birnin London

Dan ƙwallo ya dira London tare da matar sa da kuma wakilin sa don kammala shirin buga ma ƙungiyar Chelsea

Dan wasa ya iso birnin London

Dan wasan ƙasar Spain Alvaro morata ya isa london tare da matar sa Alice Campello domin shirya komawa Chelsea.

A ranar laraba 19 ga watan Yuli ne ƙungiyar Chelsea ta sanar cewa sunyi yarjejeniya kuma ƙungiyar kwallo Real madrid ta amince da siyan dan kwallon.

Morata ya iso London ranar alhamis 20 ga wata inda liƙitoci zasu gwada lafiyarsa don kammala shirin komawa Chelsea.

Dan wasan mai shekara 24 ya dira London tare da matar sa Campello da wakilin shi Juanma Lopez.

ADVERTISEMENT

Dan ƙwallon ya sanar ma sky sport cewa Antonio Conte shine dalilin zuwan sa Chelsea inda yace;

“Antonio Conte yana daga cikin manya masu horo a duniya kuma ina mai farin ciki kasancewa zan yi aiki da shi”.

A ranar laraba da ta gabata dan wasan yayi ma yan wasa da ma’aikatan ƙungiyar Real madrid banƙwana a inda suke horo a garin Los angeles.

Morata zai sa hannu a takarda na ƙwangila wanda zai dinga amsar albashin pam 155,000 a ko wani mako.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT