ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Hanyoyi 5 da mutum zai bi domin tsira daga kamuwa da cutar Monkeypox

Hakika akwai hanyoyi da mutum zai bi wajen kuɓuta da kamuwa da wannan cutar da ta ɓarke kwanan baya

Tun barkewan wannan cutar an samu mutum 30 da suka kamu da ita a fadin jihohi 7 da haka muke iya cewa hakika wata sabon annoba ta fadi a Nijeriya mai suna Monkeypox.

Dangane da rahoton da NCDC wato Cibiyar warkar da cututuka na kasa ta fitar, tun da cutar ta ɓarke a jihar Bayelsa a 22 ga watan satumba ta yaɗu har zuwa jihar Ogun, Rivers, Ekiti, Akwa ibom, Crossrivers da Lagos.

Alamun wannan cutar ya hada da matsananciyar ciwon kai, zazzabi, ciwon baya da dai sauran su.

Babban alamu mai razanarwa shine fitowar kuraje dake yaɗuwa a duka jikin mutum.

ADVERTISEMENT

Yayin da cibiyar NCDC ke neman hanyar da za’a kawar da wannan annoban, ga wasu hanyoyin da zamu iya bi domin kuɓuta daga kamuwa da wannan cutar;

1. Guje wa daga dabbobin daji irin su birai, beraye, kurege da dai sauran su

Hanyar farko da mutum ke kamuwa da wannan cutar shine daga dabbobin daji ta hanyar, cin karo da jini ko ruwan jikin dabba ko kuma ta hanyar cizo ko karta daga dabbobi. Birai, kurege da ɓera suna daga cikin muhimman dabbobi masu aikata haka.

Da haka ya kamata mutum ya sanya katangar wariya tsakanin shi da dabbobi indai yana neman tsira.

2. Mutum ya kaurace cin naman dabbobin daji wanda bai dahu ba

ADVERTISEMENT

Yayin da wasu basu iya kauracewa da cin naman ɓera ko na biri kasancewar tana da dadi. A halin yanzu dai yin haka ba abu ne mai taimakawa wajen samun sinadarurruka mai gina jiki.

Imma dai mutum baya iya kaurecewa da cin neman toh ya tabbatar neman ya dahu sosai kafin ya sanya a bakin sa.

3. Ka lura da yadda kake mu’ammala da wanda ya kamu da cutar

Hanya ta biyu da mutum ke kamuwa da wannan cutar shine daga wanda ya kamu da cutar zuwa ga wani.

Dalilin haka cibiyar NCDC ta ware wadanda suka kamu da cutar.

ADVERTISEMENT

Mutum na iya kamuwa da cutar monkeypox ta hanyar iska ko cin karo da na’yuka na daga cikin jikin wani mutum wanda ya kamu da cutar.

Nau’in ruwa na daga cikin jikin mutum dake iya yin sillar kamuwa da wannan cutar sun kunshi yawun baki, hawaye, fisari, yawun tari da ruwan dake fitowa yayin da mutum yayi atishawa

Mutum ya kiyaye kansa daga taba ire-iren nau’in ruwan jikin dan adam.

4. Kaje a baka rigakafi

A halin yanzu dai ba’a samu hanyar waraka da wanna cutar amma an kawo rahoto cewa rigakafin cutar smallpox yana iya rege tsananin cutar.

ADVERTISEMENT

5. Ka kasance kana tsabtace kanka

Yawan wanke hannu da sabulu da makamantar haka zai taimaka idan har mutum na neman tsira daga kamuwa da wannan cutar.

Tunda har yanzu cibiyar warkar da cututtuka na NCDC na kan hanyar samad da rigafi wanda zai kawar da wannan cutar a ƙasar, ya zama dole mutum ya tsirartar da kanshi daga wannan annoban wanda har yanzu babu labari mai cewa tayi sanadiyar mutuwar daya daga cikin wadanda suka kamu dashi.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT