Pulse.ng logo
Go

Rotimi Ameachi Ministan Buhari ya fallasa albashin da suke samu ko wani wata

Ministan ya bayyana cewa ko wani minista na samun N950,000 ko wani wata a matsayin albashi

  • Published:
Judges, lawyers flee court as APC crisis in Rivers deepens play

Minister of Transportation Rotimi Amaechi

(Hisprideblog )

Daya daga cikin ministocin shugaba Buhari ya fallasa adadin kudin albashi da suke karba ko wani wata.

Ministan sufurri kuma tsohon gwamnan jihar Ribas Rotimi Ameachi, ya bayyana cewa suna samun N950,000 ko wani wata a matsayin albashi.

Ministan ya bayyana  hakan ne a Abuja a taron kaddamar da sabuwar littafi da tsohon ministan ayyukan waje marigayi Mathew Mbu ya rubuta.

Ameachi  yace a cikin albashin ministocin ke cire kaso na jami'o'i dake aiki karkashin su.

"Ko wani minista na amsar albashin N950,000 ko wani wata. N350,000 daga cikin kudi na muhalli ne kuma sauran N600,000 da ya rage ciki za'a biya hadimai da sauran ma'aikata dake aiki karkashin ministan." yace.

Ministan ya kara da cewa gwamnatin shugaba Buhari ta takaita yawan badakala da jami'an gwamnati keyi da kudi.

A cewar shi an samu raguwar barnar kudi da yawan hada bukukuwa mara amfani da jami'o'in gwamnati keyi a da kasancewar rashin bude kofar badala da gwamantin yanzu ta kafa.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.