Pulse.ng logo
Go

John Mikel Obi Jagoran yan wasan Super eagles ya nuna godiya bayan kubutar da mahaifin shi da masu garkuwa da mutane suka yi

Rahotannin sun nuna cewa an sace mahaifin sa ne hanyar sa zuwa jihar Enugu dake kudancin Nijeriya daga jihar Benuwe.

  • Published:
John Mikel Obi play

John Mikel Obi

(Oleg Nikishin/Getty Images)

Jagoran yan wasan tawagar super eagles ta Nijeriya, Mikel Obi, ya mika godiyan sa ga jami'an tsaro da suka kubutar da mahaifin shi daga hannun masu garkuwa da mutane da suka sace shi.

Kamar yadda dan wasan ya bayyana, labarin sace mahaifin shi ya kai ga kunnen shi sa'o'i gabanin wasan Nijeriya da Argentina a gasar kofin duniya.

Mikel John Obi play

Mikel John Obi

(Patrick Smith - FIFA/FIFA via Getty Images)

 

Rahotannin sun nuna cewa an sace mahaifin sa ne hanyar sa zuwa jihar Enugu dake kudancin Nijeriya.

A wata takardar sanarwa da rundunar yan sanda ta jihar Enugu ta fitar, jami'an rundunar sunyi nasarar kubutar da mahaifin dan wasan ranar 2 ga watan Yuli daidai karfe 2 na rana.

Mikel John Obi's dad Pa Michael Obi play

Mikel John Obi's dad Pa Michael Obi

(Ihuoma Chiedozie)

 

Sakamakon kokarin da rundunar yan sanda suka yi, Mikel Obi ya jinjina masu tare da yi masu godiya.

Ga sakon da ya rubuta a shafin sa na twitter kamar haka "Ina mai mika godiya ga jami'an tsaro da suka kubutar da mahaifina bayan lamarin da ya faru cikin satin nan".

Bugu da kari tsohon dan wasan tawagar kungiyar Chelsea dake Ingila, ya yi dinbim yan kasa da suka taya shi jaje tare da mara masa baya.

Super Eagles captain Mikel Obi has thanked the Nigerian Police Force (NPF) for the safe return of his father who was kidnapped. play (Independent)

 

Lamarin dai shine karo na biyu da masu garkuwa da mutane suka saci mahaifin shahararren dan kwallon. Karo na farko ya faru a cikin shekarar 2011.

Tuni dai dan wasan ke ta samu jinjina da yabo daga yan kasa a kafafen sada zumunta da kafofin watsa labari bisa bajinta da ya nuna wasan Nijeriya da Argentina duk da ya san cewa anyi awon gaba da mahaifin shi.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement