Pulse.ng logo
Go

MAGNITO An raina mawakan Arewa shiyasa na kaurace zuwa Legas kuma ina nan ina daga tutar arewa - Inji fitaccen mawaki

Shahararren mawakin arewa yayi bayani game da dalilin da ya sa ya bar arewa zuwa jihar Legas domin cin moriyar sana'ar waka

  • Published:
magnito tare da Vj Adams play

magnito tare da Vj Adams

Fitaccen mawakin wakar gambara wato hip-hop ta Rap, Muhammed Adamu Usman wanda aka fi sani da Magnito yayi karin haske kan yadda ya tsinci kansa a jihar Legas da irin rawar da yake takawa a harkar nishadi.

A wannan hirar da muka yi dashi yayin da ya kawo mana ziyara, mawakakin ya bayyana yadda hausa Hip-hop ke samun cigaba da irin rawar da yake takawa wajen daga tutar Arewa.

Ya bayyana cewa burin sa shine ya zama na daya a nahiyar Afrika kuma a halin yanzu yana hanya wajen cinma burin sa.

Magnito play

Magnito

(Instagram/Magnitofreshout)

Haifafen dan jihar Benuwe, mawakin yana daya daga cikin yan arewa da akake damawa dasu a harkar nishadi a kasar.

Ga yadda hirar mu ya kasance:

Bamu takitaccen tarihin kanka?

cikin dariya.. shiyasa kaji a cikin waka ta na idan nkudin kuke so dukanku ku. Sunana Muhammed Usman Adamu. Ni dan jihar Benuwe ne amma nayi girma a Abuja, a nan naji hausan da nake yi.

Nayi karatun jami'a University of Jos. Bayan kammala karatu ne ne na kom Legas inda na fuskanci sana'ar waka din-din-din.

Yaushe ka sa a ranka cewa waka kake son kayi?

Na fara wakatun lokacin da ya shiga Jami'a. A lokacin na kan rubuta baitutka in yaga, in kara rubuta in yaga kuma a lokacin ina wakar Rap ne bisa ga so da nike ma irin salon wakar, ba wai ina yi ne domin in zama wani shahararren mawaki ba.

Lamarin ya canza bayan wata waka da nayi mai taken M.A.G.N.I.T.O, wakar ya samu karbuwa a garin Jos da kewaye. Mutane nata yaba mun tare da kira na a waya. Idan ban manta ba, wasan na farko da aka gayyace ni an biya ni naira dubu N30,000, a lokacin nayi mamakin yawan kudin kuma abun ya birge ni.

magnito tare da Vj Adams play

magnito tare da Vj Adams

Wani shekara kenan kuma yaya abun yake a wancan lokacin?

Tsakanin shekarar 2005 da 2006 ne. Daga nan kuma na fara zuwa wasanni a wurare da dama. A lokacin na kan halarci wassanin Rapbatle da freestyle cikin har da wani da mawaki M.I ke shiryawa. A lokacin ma ya kan kira ni idan zai shirya wasa domin nima inzo in nuna bajinta ta.

Wani irin kalubale ka fuskanta yayin da ka zabi yin waka a matsayin sana'a?

Ka san na fito daga gidan musulmai, kuma a sanda na fara na fuskanci kalubale sosai. kai ma ka san kai tsaye kana dan musulmi ka ce zaka yi waka, ai iyayen ba zasu goyi bayan ka ba. Iyaye na a lokacin nata tseigumi kan lamarin har ma suka kai kara ta ga kakkani na tare da shirya shirya taro ta musamman domin ja mun kunne. Wannan dalilin ma ya sa na jinkirta harkar waka a lokacin. Shiyasa ka gan sai yanzu nake kokarin tura wakoki na ga jama'a. Daga baya iyaye na sun saduda, yanzu haka mahaifiya ta itace jagora cikin dinbim masoya na. Idan na tafi gurinta yanzu, abu na farko da ke tare ni dashi idan muka ci karo  shine "If i get money", wato taken waka ta kenan. A raina sai in ce, ga wacce taki mara mun baya  a farko ta koma mai kaunar wakoki na.

mawaki dan asalin jihar Benuwe mai wakar hip-hop play

mawaki dan asalin jihar Benuwe mai wakar hip-hop

(Instagram/Magnitofreshout)

 

Kai mawakin hausa ne ko turanci?

Tun asali, ina waka ta da harshen turanci. Na kan sanya hausa cikin wasu baitutuka ko da daya ko biyu a cikin wakoki na. ai yanzu aka fara samun mawakan hausa rap, a lokacin da muka fara waka babu masu yin haka sosai. Ina saka baitutuka cikin harshen hausa ne domin su san cewa ni dan Arewa ne

Menene dalilin ka na barin Abuja?

Dalilin da ya sa na bar Abuja shina, a Abuja na gama cin moriyar basira ta. Sai da na zama daya daga cikin manyan mawaka wanda ake ji da su. Nayi kaurin suna sai dai kuma ba'a biya na yadda ya kamata. Idan an kira ni inzo inyi wasa a biki zaka gan an biya ni kamar naira dubu dari zuwa dari da hamsin amma ka gan idan an kira mawaki daga Legas a biya shi Miliyan guda ko fiye da haka. Wato kawai an raina yan gida kenan. Dalilin haka nima na yanke shawara na in koma cibiyar harkar nishadi a nahiyar Afrika wato jihar Legas domin nima inci moriyar ganga ta a sana'ar waka. Idan kayi fice a nan hakika duniya zata san da kai.

Kana ganin an samu cigaba a bangaren wakokin hausa hip-hop kuma ya jama'a ke kallo salon wakar ka?

A mana! sosai ma kuwa. Ga su Morell ga Classiq da sauran su. A gaskiya an samu cigaba. yanzu haka muna kokari wajen dora Arewa a hanya domin a dama damu a harkar.

Kana ganin ka kai matsayin da kake so a harkar waka?

Ina hanyar yanzu. Ai ya kamata a ce a Afrika nine na daya saboda irin wakoki da nake dashi. Amma ka san fitar da waka yana da tsada sosai kuma ni nake daukar nauyin yin haka da kaina. Ganin inda nake a masana'antar a halin yanzu, sai dai inyi godiya ga Ubangiji. Babu sauki gaskiya, domin komai sai da kudi. Da yardar Allah kafin shekara ya kare zamu kai wani matsayi na gaba.

Wakoki nawa kayi tunda ka fara waka?

Ah! Wallahi ban san adadin wakokin da nayi ba. Wasu lokuta idan an saka waka ta wanda nayi amma ban fitar ba, sai dinga tambaya ko ni nayi shi. Gaskiya wakoki na suna da yawa domin tun shekarar 2003 nake shiga studiyo. Akwai wani waka da nayi tun a baya, yanzu haka ina shirin fitar dashi tare da Tuface haka kuma akwai wani da nayi da Wande Coal

Wani aiki kake shiryawa yanzu?

Ina shirin fitar da kundin waka ta na farko. Bayan haka zan sake fitar da EP da Loss Tape da mixtape domin cikin shekarar nan ina son in fitar da wakoki akalla su 30

Ka taba yin waka wanda gaba dayan ta cikin harshen hausa aka yi ta?

A, akwai wani waka da nayi ma arewa sai dai wakar sautin sa ya kasa ba irin yadda nake fitar da sauran wakoki na ba. Yanzu haka ina shirin yin wata waka ma arewa bayan na fitar da album

Wani yanki na Nijeriya kake ganin ka fi samun masoya?

Ina iya cewa kaso 100 na masoya na yan Arewa ne musamman yan abuja. Sai dai amma akwai masoya na a sauran wurere na Nijeriya, Warri, Portharcourt da sauran su.

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.