Pulse.ng logo
Go

Hindatu Maizabo An daura auren matashiya, tsohuwar shugabar karamar hukuma mafi karancin shekaru(hotuna)

Matar shugaban kasa Aisha Buhari da uwargidan gwamnan jihar Kebbi, Hajiya Zainab Atiku Bagudu sun halarci bikin auren wanda aka gudanar a garin Argungu

  • Published:
Amarya Hindatu tare da matar gwamnan jihar Kebbi, Dakta Zainab Atiku Bagudu play

Amarya Hindatu tare da matar gwamnan jihar Kebbi, Dakta Zainab Atiku Bagudu

(Facebook/rariya)

Matashiya, Hindatu Maizabo wanda ta rike mukamin shugaban karamar hukumar Argungu dake jihar Kebbi..

An daura auren ta da ango, Abubakar Musa ranar juma'a ga watan mayu a garin Argungu.

An daura auren ta ga ango Abubakar Musa ranar juma'a 4 ga watan mayu play

An daura auren ta ga ango Abubakar Musa ranar juma'a 4 ga watan mayu

(facebook/rariya)

 

Uwargidan gwamnan jihar Kebbi, Hajiya Zainab Atiku Bagudu ta halarci bikin auren ta tare da wakilan matar shugaban kasa wanda Hajiya Fatima Rafindadi ta jagoranta.

Kamar yadda jaridar Rariya ta fitar, uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ta bada gudummawa ga sabuwar amaryar.

Tawagar uwargidan shugaban kasa da matar gwamnan Kebbi tare da ma'auratan play

Tawagar uwargidan shugaban kasa da matar gwamnan Kebbi tare da ma'auratan

(Facebook/rariya)

 

Hindatu ta rike mukamin shugabar karamar hukuma na rikon kwarya ne a cikin shekarar 2016. Matsayin ta tada kura tare da janyo tseigumi da cece-kuce ga al'ummar jihar Kebbi da ma sauran kasashen nijeriya.

Ta rike mukamin tana da shekara 25 a duniya bayan wa'adin asalin wanda ke rike da mukamin ya kai karshe.

Ta kafa tarihi na zama mace a farko mai karancin shekaru da ta rike mukamin shugabancin karamar hukuma.

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.