Pulse.ng logo
Go

Allah wadaran Kan dalilin kishi matashi yayi ma budurwar sa yankan rago

Yace ya yanke shawarar aikata mumunar laifin ne bayan da ya nemi iyayen sa da su je su nema masa auren Hauwa amma sunki, wanda kuma daga bisa sai ya gan wani matashi irin sa ya fara zuwa wajen ta, ganin haka ya aikata laifin domin kowa ma ya rasa.

  • Published:
Matashi yayi ma budurwar sa yankan rago a jihar Yobe play

Matashi da yayi ma budurwar sa yankan rago

(rariya)

An samu labari mara dadi daga jihar Yobe inda ake zargin wani matashi mai suna Muhammed Isa Adamu da yi ma budurwarsa yankan rago.

Lamarin ya faru a karamar hukumar Potiskum na jihar ranar 29 ga watan mayu.

Kamar yadda rahoto ya bayyana, iyayyen budurwar mai suna Hauwa sun yi ta cigiyar ta bayan da suka aike ta zuwa shago mafi kusa dasu siyan buredi da zasu karya kumalo dashi.

Bayan kai-kawo da suke tayi zuwa kafofin watsa labarai da bada cigiyar ta a wurin yan sanda da gidajen telebijin bayan shafe sa'o'i da dama sai suka ji labarin an tsinci gawar ta a daidai titin Gujba.

Kamar yadda majiya Rariya suka ruwaito, matshin wanda ake zargi da aikata laifin ya shaida wa manema labarai cewa ya gayyaci Hauwa tsohuwar budurwarsa wadda ya fara nemanta tun 2014, soyayyarsu tayi nisa sosai, kuma bai taba sa ta wani abu ta ki yi ba, ya tabbatar da irin biyayya da Hauwa take masa, wannan dalilin yasa da ya gayyace ta kan hanyar Gujba, ba ta yi masa jayayya ba.

A cewar sa, bayan sun gama hirar su da Hauwa, sai ya umarce ta da ta rufe idonta, ba ta yi jayayya ba nan take ta rufe idon ta ba tare da ta san me yake shirin yi mata ba, sai ya ciro wuka ya soke ta a wuya, bada wani bata lokaci ba rai ya yi halinsa.

Yace ya yanke shawarar aikata mumunar laifin ne bayan da ya nemi iyayen sa da su je su nema masa auren Hauwa amma sunki, wanda kuma daga bisa sai ya gan wani matashi irin sa ya fara zuwa wajen ta, ganin haka ya aikata laifin domin kowa ma ya rasa.

Yan sanda sun cika hannu dashi kuma kamar yadda kwamishnan yan sandan jihar Yobe ya shaida wa manema labarai za'a gurfanar dashi gaban kotu don yanke masa hukunci.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.