ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Fusatattun matasa sun far ma ofishin yan sanda, sun kone motoci da dama

Matasan sun kai farmakin ofishin da sharadi na a mika masu yan ta'adda uku da ake zargi da kai hari kauyen Mashema da aka kama.

Matasan sun kai farmakin ofishin yan sandan shiyar yammacin ranar asabar inda suka bukaci jami'an yan sanda su mika masu yan ta'adda uku da rundunar sojoji suka mika masu.

Kakakin rundunar yan sanda na jihar SP Muhammed Shehu ya tabbatar da faruwar haka ga manema labaru a garin Gusau ranar lahadi.

Kakkakin yace matasan sun kone wasu motoci da babura dake ofishin.

ADVERTISEMENT

Yace matasan ggarin sun far ma ofishin jami'an tsaro ne bayan sun samu labari cewa an mika wasu yan ta'adda uku da ake zargi da kai hari kauyen Mashema na karamar hukumar ranar 6 ga watan Yuli.

SP Muhammed Shehu ya kara da cewa da kyar jami'an dake ofishin suke kubuta daga fushin matasa inda yace ta kangon dake bayan ofishin suka tsallaka domin neman tsira.

Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya kara da cewa kura ta lafa game da batun kuma an mika yan ta'addan da ake zargi ga babban ofishin rundunar na jihar domin cigaba da bincike.

Al'ummar Zurmi na zama cikin halin fargaba da tashin hankali sakamakon hare-haren da yan ta'adda ke kai masu.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT