Pulse.ng logo
Go

Zaben fidda gwani Mata biyu da suka yi nasarar samun tikitin APC na takarar Sanata a jihar Adamawa

MATA BIYU SUN SAMU NASARAR ZAMAN YAN TAKARAR SANATA KARKASHIN APC - Sanata Binta Masi da Hajiya Hajiya Aisha Dahiru 'Binani' sune matan da zasu fito takarar majalisar dattawa karkashin jam'iya mai mulki ta APC a jihar Adamawa.

  • Published:
Senarto Binta Garba Masi play Sanata Binta Garba Masi (Daily Nigerian)

A jihar Adamawa wasu mata biyu sun jajirce kuma sunyi nasarar samun tikitin jam'iyar APC na takarar majalisar dattawa.

Sanata Binta Masi wacce take daya tilo daga arewacin Nijeriya dake zauren majalisar dattawa tayi nasarar samun tikitin sake tsayawa takara domin wakiltar al'ummar yankin arewacin jihar Adamawa.

Ta samu tikitin cikin ruwan sanyi bayan rashin samun abokin takara mai neman kujerar.

Ita ma tsohuwar yar majalisar wakilai daga jihar, Hajiya Aisha Dahiru, zata nemi zarcewa zuwa zauren majalisar dattawa bayan da ta lashe zaben fidda gwanin da jam'iyar APC tayi.

Yar majalisar wacce aka fi sani da Binani doke maza hudu da suka fito takara da ita wajen zama gwanin APC wacce zata kara a zaben 2019 domin wakiltar jama'ar yankin Adamawa ta tsakiya.

Zata nemi ta maye gurbin mai wakiltar yankin, Sanata Abdul-Azeez Nyako, wanda ya sauya sheka daga APC zuwa jam'iyar ADP kuma wanda ke neman zaman gwamna a zaben 2019 karkashin sabon jam'iyar da ya koma.

Ta samu kuri'u 1, 282 yayin da mai binta a baya, Alhaji Wakili Boya, ya samu kuri'u 599 na kuri'un da aka kada.

Shima dan majalisa mai wakiltar kudancin jihar Adamawa karkashi jam'iya APC, Sanata Ahmed MoAllayidi, ya samu tikitin tsayawa takara cikin ruwan sanyi.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement