Pulse.ng logo
Go

Maryam Sanda Maryam ta mayar da martani kan hotunan bikin cikam shekara na diyar ta

Tayi kira na a daina saka diyar ta cikin cece-kuce da ake yi kan batun ta a kafafen sada zumunta

  • Published:
Tsohon hoton Maryam da diyar ta sanda take jaririya play

Tsohon hoton Maryam da diyar ta sanda take jaririya

(Instagram/tozali)

Kan hotunan da yayi yawo kwanan baya na bikin cika shekara daya na diyar su, Maryam sanda wanda ake tuhuma kan zargin kashe mijinta ta mayar da martani kan tsokacin da jama'a suka yi a kafafen sada zumunta kan hotunan.

Tayi karin haske kan labarin da muka fitar kwanan baya na hotunan bikin cika shekara daya na diyar su Aleesha wanda yayi yawo a yanar gizo.

Wasika da yar uwar ta Aisha Sanda ta aika ma jaridar Vanguard,tayi magana a madadin iyalin su kan batun hotunan da ya janyo cece kuce inda jama'a ke zargin ta da nuna halin ko-in kula kan laifin da ake zargin ta dayi.

Aisha Sanda tayi karin haske inda ta bayyana cewa hoton Maryam da diyar ta wanda aka gani ba na kwanan nan bane kuma wanda aka gan  diyar tare da kek cikin dakin da aka yi ma ado ba biki bane. Tace mahaifiyar su ta bada umarni na a yi hakan.

Bikin cika shekara da Maryam Sanda ta hada ma diyar ta play

Bikin cika shekara da Maryam Sanda ta hada ma diyar ta

(Instagram/tozali)

 

Tayi karin haske inda tace a bisa al'adar gidansu ko wani wata ake daukar hoton diyar amma sai dai tun watan Yuli na bara aka samu damar yin haka sanadiyar taqaddamar da ita maryam ke fuskanta a kotu.

Tace an dauki hotunan ne ba tare da yin biki kamar yadda labari ya yadu don samun hotunan tuna baya na cika shekara daya na diyar.

An tura hotunan diyar ga yan uwan mahaifinta dake jihar Kebbi don ganin yadda diyar su ta raya wannan ranar. Aisha tace tayi mamakin yadda hotunan suka yadu a kafafen sada zumunta.

"Muna Sane cewa kowa na bukatar adalci kan karar da aka shigar, haka zalika muma muna jiran hakan  amma muna kira da a cire diyar cikin lamuran manya kan batun yayin da mahaifiyar ta fuskantar tuhuma" ta kara.

Tsokacin jama'a

Jama'a sunyi tsokaci kasancewa lamarin ya faru kwanan biyu bayan hukuncin da kotu ta zantar na bata damar yin beli.

Maryam ta samu damar bayan rokon da alkalin ta yayi bisa barazanar da take fuskanta na rashin lafiya sakamakon juna biyu da take dauke dashi na wata uku.

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement